Daga DAUDA USMAN a Legas
A Legas, kwamitin majalisar matasan Hausawa na unguwar F-Shor da ke ƙaramar hukumar Kuje Amuwo Odofin, ƙarƙashin jagorancin Sarkin Samari Alhaji Tijjani Abdulrahman, ya gudanar da gagarumin taron nuna wasannin gargajiya, domin farfaɗo da al’adun Bahaushe tare da wayar da kan matasa mazauna yankin.
Taron, wanda aka gudanar a makon da ya gabata, ya haɗa matasa daga sassa daban-daban na unguwar F-Shor, tare da halartar ’yan kabilu iri-iri. An gudanar da fitattun wasannin gargajiya irinsu damben gargajiya, kokowa, wasan kwai-kwayo, langa da sauran su — duk a matsayin nuni ga al’adun Hausawa na Arewa.
Da yake magana da Blueprint Manhaja a Legas, Sarkin Samarin, Alhaji Tijjani Abdulrahman, ya bayyana cewa manufar shirya taron ita ce karfafa al’adun gargajiya ga ’ya’yan Hausawa da aka haifa a Legas da sauran mutanen da ke zaune a yankin. Ya ce wannan mataki zai taimaka wajen tabbatar da cewa matasan ba su manta da asalin al’adun iyayensu ba.
A yayin taron kuma, matasan sun taya ɗan uwansu, Alhaji Abdullahi Muhammad, murnar sabon aure da ya yi da amaryarsa Malama Maryam Yakubu, wanda aka daura masa a makon da ya gabata.
Mambobin kwamitin matasan da suka jagoranci shirya taron sun haɗa da: Sarkin Samari Alhaji Tijjani Abdulrahman, Abdullahi Muhammad, Auwalu Shehu Adam Goje, Ali Dan Tsugudi, Kamaluddeen Adamu da wasu.
Sarkin matasan ya yi kira ga Hausawan da ke zaune a Legas da sauran jihohin Kudu maso Yamma da su rika gudanar da irin waɗannan wasanni domin kare al’adunsu da kuma koyar da matasa muhimmancin gadon halitta. Ya kuma shawarci matasa su dage wajen neman ilimi da koyon sana’o’in hannu domin kauce wa tsanantuwar rayuwa.
A ƙarshe, ya yaba da irin jagorancin da Mai Martaba Sarkin Hausawan F-Shor da Magajin Garin F-Shor ke yi, yana mai cewa suna tafiyar da al’umma cikin gaskiya da adalci.
