Yadda ‘yan kasuwar Mile-12 a Legas suka gudanar da addu’o’in nema wa Nijeriya zaman lafiya 

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

A Legas, an gudanar da taron addu’o’i na musamman a kasuwar Mile 12 International Market ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban kasuwar, Alhaji Isa Muhammad Mai Shinkafa, tare da babban sakataren kasuwar, Alhaji Balarabe Idris. Taron ya mayar da hankali ne kan neman zaman lafiya da bunƙasar Nijeriya.

Taron, wanda ya samu halartar manyan malamai magada Annabaw daga sassa daban-daban na Legas, ya gudana cikin natsuwa da tsari.

A farkon taron an raba malaman gida uku, inda kashi na farko suka karanta ayoyi masu tsarki na Al-Kur’ani, kashi na biyu suka gudanar da addu’o’i na musamman, yayin da kashi na uku suka ci gaba da roƙon Allah domin zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar.

Bayan kammala addu’o’in, an gudanar da ɗaura auren ɗan kasuwar ɓangaren citta da tafarnuwa, Alhaji Usaini Danladi Kofa, da amaryarsa Aisha Amira Usaini Sarki, a bainar jama’a. Mahalarta taron sun taya ma’auratan murna tare da yi musu fatan alheri.

Da yake jawabi, tsohon shugaban dattawan kasuwar Mile 12, Alhaji Isa Muhammad Mai Shinkafa, ya godewa mahalarta bisa halarta taron, tare da yi wa al’umma fatan alheri da komawa gidajensu lafiya. Ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin mataki na ƙara haɗa kan jama’a da kuma neman albarkar Ubangiji ga ƙasar.

A nasa ɓangaren, babban sakataren kasuwar, Alhaji Balarabe Idris, ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da tsaftar muhallin kasuwanci. Ya yi kira ga ’yan kasuwa su ci gaba da yin aiki tare domin bunƙasa harkokinsu da kuma kyautata zaman lafiya a kasuwar.

Angon da aka daura masa aure, Alhaji Usaini Danladi Kofa, ya yi godiya ga shugabannin kasuwar bisa irin goyon bayan da suke ba wa ’yan kasuwa. Ya kuma yaba da ƙoƙarin shugabannin wajen haɓaka haɗin kai da samar da yanayi mai kyau ga kasuwanci, inda ya roki ’yan kasuwa su ci gaba da mara wa shugabancin kasuwar baya domin cigaba da samun sauƙin gudanar da harkoki.

By ukarofi