Yadda matashiya mai sikila ta rasu shekara guda bayan kammala digiri

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata matashiya ’yar Nijeriya kuma mai fafutukar wayar da kai kan cutar sikila, Anisa Ishaƙ-Balogun, ta rasu shekara guda kacal bayan ta kammala karatun digiri na farko da sakamako mafi girma a jami’a.

Marigayiyar, wacce aka fi sani da sunan @Nerdy_neesah a dandalin sada zumunta na ɗ, ta rasu ne ranar Laraba bayan shafe shekaru tana fama da cutar Sikila.

Rahotanni sun nuna cewa marigayiyar ta kasance mai jajircewa wajen karatu duk da ƙalubalen rashin lafiya da take fuskanta.

A shekarar 2025, ta kammala karatun digiri na farko a fannin Cell Biology and Genetics daga Jami’ar Jihar Legas, inda ta samu sakamakon First Class da matsakaicin maki na 4.82 daga cikin 5.00.

Anisa na daga cikin ɗalibai 14 da suka samu irin wannan matsayi na farko a zangon karatu na shekarar 2023/2024 a jami’ar. Duk da kasancewarta cikin yanayin rashin lafiya a wasu lokuta, an ruwaito cewa sau da dama tana rubuta jarrabawarta ne daga asibiti.

Sanarwar rasuwarta ta fito ne daga wani mai amfani da dandalin ɗ mai suna @dhareymu, wanda ya rubuta cewa an yi jana’izarta a safiyar ranar bayan rasuwar, tare da kira ga jama’a da su yi mata addu’a.

A saƙon nasa ya ce: “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. A taimaka a yi mata addu’a idan kuka ga wannan saƙon. Allah Ya gafarta mata kura-kuranta, Ya yalwata mata kabari, Ya kuma sanya ta cikin mazauna Aljanna.”

Mutuwarta ta jawo alhini a tsakanin abokai, ɗalibai da masu bibiyar ta a kafafen sada zumunta, inda da dama suka bayyana cewa labarin rasuwar ya girgiza su musamman ganin irin gwagwarmayar da ta yi wajen haɗa karatu da jinyar cutar sikila.

Rahotanni sun nuna cewa nasarar da ta samu a karatu ta samu ne sakamakon jajircewarta da kuma goyon bayan iyalanta, musamman mahaifiyarta wacce ta kasance tana ƙarfafa mata gwiwa a duk lokacin da cutar ta taso mata.

Masu sharhi sun bayyana cewa rayuwar Anisa ta kasance abin koyi ga matasa da dama, domin ta nuna cewa ƙalubalen lafiya ba dole ba ne su zama katanga ga neman ilimi da cimma buri.

Rasuwarta ta kuma sake tayar da muhawara kan muhimmancin tallafi da kulawa ga masu fama da cutar sikila a Nijeriya.

By ukarofi