
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan jaridar Al-Jazeera, Mehdi Hassan ya fitar da wani faifan bidiyo a matsayin hujja akan mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Daniel Bwala game da wasu kalamai da ya yi a baya na sukar Shugaba Bola Tinubu.
A wata hira ta shirin Hassan mai suna Head to Head, Bwala ya musanta furta kalamai na sukar Tinubu a baya, inda kwatsam sai aka haska masa wani bidiyo da yake yin irin kalaman akan shugaban ƙasar.
Hassan ya yi tsokaci ne akan zarge-zargen da Bwala ya yi a baya na cewa Shugaba Tinubu ya samar da wasu ‘yan daba domin yaƙar ‘yan adawa da kuma yunƙurin halaka shi.
Saidai a yayin haka ne Bwala ya musanta waɗannan ikirarin, lamarin da ya sa ɗan Al-Jazeerar ya gaggauta sake bidiyon da ke nuna shi a lokacin da yake yin furucin. Haka kuma akwai wasu hujjoji da Hassan ya yi amfani da su wajen tutsiye Bwala.
Wannan hira ta haddasa cece-kuce da sukar Bwala, inda ‘yan Nijeriya da dama suka riƙa kira na a tsige shi daga muƙaminsa a gwamnatin Tinubu.
Masu sukar sa sun ce rashin tsare aiki ga Bwala yadda ya dace tuzarci ne ga gwamnatin Tinubu da ma Nijeriya a matsayinta na ƙasa.
