Trump ya yi barazanar faɗaɗa hare-hare yayin da Iran ta ci alwashin ƙin ajiye makamai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Donald Trump na Amurka ya gargaɗi Iran da cewa za za fuskanci munanan hare-hare daga yanzu.

Ya kuma yi barazanar cewa Amurka za ta faɗada hare-harenta a ƙasar zuwa sabbin wurare da nufin abin da ya kira da ”kammala wargaza ƙasar”.

Trump ya kuma yi zolaya ga afuwar da Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya nema ga maƙwabtan Iran saboda hare-haren da ƙasarsa ta kai musu a tsawon makon da ya wuce.

Shugaban na Amurka ya bayyana alƙawarin daina kai wa maƙwabtan Iran hari da Mista Pezeshkian ya yi – muddin ba a ƙara kai mata hari daga cikin su ba a matsayin miƙa wuya daga ƙasar.

Jim-kaɗan bayan jawabin Mista Pezeshkian ne dai Ƙatar ta sanar da daƙile harin makami mai linzami, yayin da ita ma UAE ta sanar da kakkaɓo wasu makamai masu linzami guda 15.

A yanzu dai an shiga mako na biyu da ake gwabza yaƙin tsakanin Amirka da Isra’ila a gefe guda da kuma Iran, wanda a farkonsa ne aka halaka jagoran addinin ƙasar, Ali Khamenei.

By Babaji