Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mazauna Jihar Kano na ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsadar sufuri, yayin da motocin bas-bas guda 222 da Gwamnatin Tarayya ta bai wa jihar domin rage kuɗin mota suka shafe watanni bakwai ba tare da fara jigilar fasinjoji ba. Wannan na faruwa ne duk da cewa an ƙaddamar da motocin a matsayin wani muhimmin shiri na rage raɗaɗin tsadar rayuwa da inganta harkokin sufuri.
Wani bincike na musamman da jaridar PREMIUM TIMES ta gudanar ya gano cewa har zuwa farkon watan Nuwamba, babu ko guda ɗaya daga cikin motocin da aka ƙaddamar a ranar 14 ga Mayu, 2026, da ya fara aiki a birnin Kano.
Motocin da aka samar ƙarƙashin shirin amfani da iskar gas ta CNG da motocin lantarki sun haɗa da bas-bas 10 masu amfani da CNG, biyar masu amfani da CNG da man fetur, motoci bakwai masu amfani da lantarki da kuma babura masu ƙafa uku 200 masu amfani da CNG.
An ƙaddamar da su ne domin rage kuɗin sufuri, bunƙasa amfani da makamashi mai tsafta da samar da ayyukan yi, musamman bayan cire tallafin man fetur da ya haddasa tashin farashin sufuri. Da yake tabbatar da rashin fara aikin motocin, Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Haruna Isa Dederi, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an kawo motocin jihar, amma ba su fara aiki ba.
Ya bayyana cewa, gwamnati ta fahimci motocin guda 222 ba su wadatar da buƙatun sufuri na jihar ba, don haka ta yanke shawarar sayen wasu ƙarin motoci. A cewarsa, an riga an sayi ƙarin motoci guda 500. Sai dai bai bayyana lokacin sayensu, inda aka ajiye su ko kuma lokacin da za a fara amfani da su ba. Haka kuma, ya ƙi bayyana inda aka ajiye motocin farko guda 222. Wannan ya bar tambayoyi kan yadda gwamnatin ke kula da motocin da aka bai wa jihar da kuma lokacin da jama’a za su fara amfana da shirin.
A wani ɓangaren kuma, gwamnatin jihar na nazarin shawarar wasu masu zuba jari daga Chana da ke son samar da babura masu amfani da lantarki guda 500, tare da gina tashar caji guda ɗaya.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Sufuri ta jihar, Zahraddeen Ibrahim, ya ce an miƙa shawarar ga kwamishinan, wanda zai gabatar da ita ga gwamna domin nazari. Ya bayyana cewa gwamnati za ta samar da filin gina tashar, yayin da masu zuba jarin za su samar da na’urorin caji. Sai dai har yanzu wannan shiri shawara ce kawai, domin ba a tabbatar da amincewar sayen motocin ko fara aiwatar da aikin ba.
A halin da ake ciki, Gwamnatin Tarayya na ci gaba da faɗaɗa cibiyoyin samar da iskar gas ta CNG a Kano. An ƙaddamar da wasu tashoshin cika iskar gas guda biyu da cibiyar sauya tsarin motocin a watan Oktoba, yayin da a ranar 11 ga Nuwamba aka ƙaddamar da wasu cibiyoyi guda uku da ke sauya LNG zuwa CNG.
Duk da haka, ƙarin tashoshin CNG ba zai tabbatar da raguwar kuɗin mota kai tsaye ba, matuƙar ba a samar da motocin da za su yi amfani da makamashin ba, tare da tabbatar da cewa masu sufuri suna mayar da rangwamen kuɗin mai ga fasinjoji.
