Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon Shugaban Nijeriya na gwamnatin mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya bayyana cikakken bayani game da aurensa da matarsa marigayiya, Maryam Babangida, ciki har da musuluntarta, a cikin sabon littafin tarihin rayuwarsa mai suna ‘A Journey in Serɓice’.
Littafin, wanda aka ƙaddamar a Abuja ranar Alhamis ta makon jiya tare da ƙaddamar da tallafin karatu gina ɗakin karatu na Fadar Shugaban ƙasa a Minna, ya bayar da haske kan labarin soyayyarsu tun daga farko a garin Kaduna zuwa rayuwarsu ta aure.
Janar IBB ya tuna haɗuwarsa da Maryam, wadda a lokacin ake kiran ta da Maria Okogwu, tun suna da ƙurucciya a lokacin da yake zaune a ɓangaren ruku’in gidajen jami’an sojoji marasa aure a kan titin Kanta da ke Jihar Kaduna.
Ya kwatanta yadda kyawunta ya birge shi, ya kira ta da “kyakkyawa” yayin da ta yi wani murmushi mai ban sha’awa.
Dangantakar su ta ɗore duk da horon da ya yi na soja a ƙasashen waje a Indiya da Ingila, kuma yakan ziyarce ta a gidan babban amininsa kuma ƙaninsa, Garba Duba.
Babangida yana da shekaru 28, bayan ya tsallake rijiya da baya a fagen fama, Babangida ya yanke shawarar natsuwa ya yi aure.
Yayin da ya ke samun sauƙi daga raunin da ya samu a ƙirji a asibitin koyarwa na jami’ar Legas, yana yawan tunanin dangantakarsa da ita, yana ganin cewa yanzu lokaci ne da ya kamata ya auri Maryam.
Ya ce, “Na zauna da Mariya a matsayin matar da zan aura kafin a sallame ni daga asibiti, kuma daga sallata, na nufi Kaduna, inda ta ke zaune tare da mahaifiyarta da kawunta. Na ƙosa in yi mata bishara: Na yanke shawarar cewa za mu yi rayuwa tare. Na yaba da ita matuƙar hankalinta.
“Ina so in sanar da ita niyyata kuma ina tsoron kar da ta ce a’a a matsayin amsa. Ci gaba a rayuwa sai da mai ƙarfin hali, kuma na yi sa’a; Har yanzu ina kallon kaina a matsayin mutum mai sa’a. Da farko, Mariya ta kasance da shakku sosai game da aurena.
“Ta san cewa ina da wani tarihi na daban, kuma waɗannan ba halayen da take so ba ne a namijin aure.”
Babangida ya bayyana cewa imani ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarsa, kuma ya buaaci Maryam ta Musulunta kafin su yi aure.
A cewarsa, “hakan bai yi wa Maryam wahala ba, wadda ke da ƙarfi a addinin Kiristanci. Na gaya mata gaskiyar cewa zan buƙaci ta Musulunta.
“Godiya ta tabbata ga Allah; wannan ba ta zama shawara mai wahala ba ga Mariya. Da yake ta kasance ‘yar Kiristoci da Musulmi a lokaci guda, kuma ta riga ta zauna a gidan Musulma. Ta karɓi Musulunci ba tare da wani gardama ba.”
Ya ƙara da cewa: “Ta rungumi rayuwar aure a matsayinta na Musulma,” inji shi.
Babangida ya kuma ba ta tabbacin ba zai auri wata mace ba, matakin da ya yi imanin ya taimaka wajen ƙarfafa aurensu.
Ma’auratan sun yi aure a ranar 6 ga Satumba, 1969, kuma sun haifi ‘ya’ya huɗu – Aisha, Muhammad, Aminu, da Halima.
Maryam ta rasu ne sakamakon ciwon daji a birnin Los Angeles a ranar 27 ga Disamba, 2009, tana da shekaru 61.
