Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
ƙasar Amurka ta fitar da jerin ƙasashen da suka cancanci shirin bayar da Biza kyauta na 2025, da ake kira ‘Waiɓer’.
Daga cikin sauran ƙasashen Afirka, Nijeriya, Afirka ta Kudu, da Ghana ba sa cikin jerin sabbin shirin ba da Biza na 2025 yayin da ƙasar ke gabatar da sabbin tsare-tsare kan cancantar Bisa.
Kwanan nan Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da sabunta shirin Bisa ta 2025 (ɓWP), wanda ke nuna jerin ƙasashen da suka cancanta da sabbin manufofin balaguron.
Wannan shiri zai sauƙaƙa shiga Amurka ba tare da biza ba ga miliyoyin mutane a duniya, kuma zai sauƙaƙa kasuwanci, yawon shaƙatawa, da tafiye-tafiye mafi sauƙi.
Shirin yafe bizar na 2025 ya haɗa da ƙasashe 40 waɗanda a yanzu ‘yan ƙasar za su iya zuwa Amurka ba tare da biza ba.
A cewar gidan yanar gizon Ofishin Jakadancin Amurka, Shirin Waiber na Biza yana bai wa ’yan ƙasashen waje damar balaguro zuwa Amurka don yawon buɗe ido ko kasuwanci har na tsawon kwanaki 90 ba tare da samun Biza ba.
