Sojoji na buƙatar tallafi domin kama Bello Turji da sauran ‘yan ta’adda – Matasan Arewa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata ƙungiyar mai zaman kanta ta Matasan Arewa Maso Yamma Mai Son Zaman Lafiya da Ci Gaba (NWYPD), ta yi kira ga al’ummar yankin da su bai wa rundunar soji boyon baya domin sake murƙushe Bello Turji da sauran ‘yan ta’adda a yankin.

Kodinetan ƙungiyar, Salihu Bello ne ya yi wannan kiran yayin da yake zantawa da manema labarai ranar Laraba a Abuja.

Bello ya kuma buƙaci jama’a da su nuna godiya ga rundunar sojojin Nijeriya bisa namijin ƙoaarin da suke yi na daƙile ayyukan Bello Turji da sauran ’yan bindiga.

“Sojoji na buƙatar mu don dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma.

“Yayin da yankinmu ke neman hanyoyin ci gaba ta fuskar tattalin arziki, a nan muna fama da dakarun koma baya, mutanen da ba sa son yankinmu ya samu ci gaba.

“Abin takaici mutanenmu ne. Ta yaya hakan ta faru? Su wane ne mutanen da ke tallafa musu kai tsaye ko a fakaice?

“Matasan Arewa maso Yamma masu neman zaman lafiya da ci gaba sun yaba wa Janar Christopher Musa wanda ya jagoranci rundunar sojin Nijeriya bisa abin da aka yi na maido da zaman lafiya a yankinmu.

“Mun sake yin kira ga mutanenmu da su tallafa wa sojoji,” inji shi.

By ukarofi