’Yan Nijeriya ba su son biyan haraji amma suna son gwamnati ta yi musu komai – Akpabio

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya yi kakkausar suka ga ‘yan Nijeriya, inda ya ce kashi 30 cikin 100 ne ke biyan haraji ga asusun gwamnatin tarayya, amma kowa na son ganin gwamnati ta samar da mafi kyawon ababen more rayuwa, ilimi da tsaro da dai sauransu.

Da yake jawabi a ranar Litinin yayin da yake bayyana buɗe taron jin ra’ayin jama’a kan ƙudirin sake fasalin haraji da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya miƙa wa majalisun biyu a ranar 3 ga watan Oktoba, 2024, ya ce sake fasalin haraji ya zama dole domin ba za a iya ci gaba da tafiya a haka ba.

A cewarsa, idan aka zartar da ƙudirorin, majalisar za ta inganta yadda take kula da gwamnati domin tabbatar da an kashe dukiyar da aka samu ta hanyar da ta dace.

A cewarsa, kamata ya yi a yi amfani da taron jin ra’ayin jama’a wajen ganin Nijeriya ta gyaru, kamar yadda ya ba da tabbacin cewa zai zauna na tsawon kwanaki biyu, ya kuma shiga cikin wannan aiki, domin ya yaɗa a kafafen sadarwa na zamani, inda zai nanata cewa mafi yawan shugabannin ƙasar nan ba su taɓa ganin abin da ƙudirin ya ƙunsa ba, wanda hakan ya sa suke kai farmaki kan tsarin.

Akpabio ya buƙaci mahalarta taron da ’yan Nijeriya da su samu kwafin takardun kuɗi kuma su gani da idanunsu maimakon dogaro da kafafen sada zumunta.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Ministan Kuɗi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Lateef Fagbemi (SAN), Shugaban Hukumar Harajin Haraji ta Tarayya, Zacch Adedeji, Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam ta Nijeriya, NSC.

Tun da farko a jawabinsa na buɗe taron, shugaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin kuɗi, Sanata Sani Musa (APC, Neja ta Gabas) ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a tattauna kan ƙudurin dokar kafa hukumar tattara kuɗaɗen shiga da kuma dokar ayyukan tattara kuɗaɗen shiga ta Nijeriya.

A cewarsa, kwamitin ya gayyaci ‘yan Nijeriya da suka haɗa da ƙungiyoyin masu ruwa da tsaki guda 71 domin jin ra’ayoyin jama’a, inda ya ƙara da cewa, “Majalisun dattawa da na wakilai sun yi karatu na biyu kan ƙudirin sake fasalin haraji kuma a shirye suke domin jin ra’ayoyin jama’a.

“Duk ‘yan kwamitin sun karanta takardun ƙudirin ne tare da fahimtar abin da ake nufi da su, kamar a fannin kula da haraji, tarawa da kuma ayyuka a Nijeriya.

“Babban maƙasudin ƙudirin yin sake fasalin haraji shi ne ganin yadda gwamnati za ta samar da ƙarin kuɗaɗen shiga ta yadda za mu samu damar ɗora ƙasarmu kan turbar ci gaban tattalin arziki inda za a kula da ababen more rayuwa, ilimi, fannin noma da kusan duk wani fannin da ya shafi yanayin tattalin arzikin ƙasa,” inji Musa.

By ukarofi