Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Biyo bayan ƙaratowar wata mai falala na Azumin Ramadana, Shugaban Hukumar Tace Fina-finai da ɗab’i ta JIhar Kano, Alh Abba El-mustapha ya bada umarnin rufe dukkannin gidajen Gala da sauran wuraren wasanni a Jihar Kano har zuwa kammala ibadar ta Azumi.
A jawabinsa, yayin kafa wani kwamitin na karta kwana ƙarƙashin Mal. Nasiru (Shehi), Abba El-Mustapha ya ce aikin wannan kwamitin shi ne ya tabbatar da babu wani gidan wasa a Jihar Kano da suke gudanar da wasa a lokacin Azumi, ya yayin da Abba El-Mustapha ya sha alwashin yin hukunci mai tsauri ga duk mai gidan wasan da aka samu gidansa da karya wannan doka.
Kazalika ya ce, wannan umarnin ya haɗa da hana dukkannin ‘yan wasa zama a gidajen wasanninsu tsawon wannan lokaci na Azumi har zuwa kammala Ramadana.
Daga ƙarshe dai ya yi kira ga ƙungiyar masu gidajen wasannin ta Gala da su saka ido sosai ga ‘ya’yan ƙungiyar tasu domin tabbatar da sun yi biyayya ga wannnan sabon umarnin.
Sannan Abba El-mustapha godewa malamai tare da al’ummar Jihar Kano dangane da shawarar da suke ba shi tare da nuna goyon bayansu a gare shi tsawon lokaci tun fara aikinsa a matsayin sabon Shugaban Hukumar ta tace fina-finai a Jihar Kano.
