Tajuddeen zai gwangwaje mazaɓarsa da manyan makarantu

Spread the love

Daga MOH BELLO HABIB a Zariya 

Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, Rt Hon. (Dr.) Abbas Tajuddeen, Iyan Zazzau, ya yi alƙawarin samar da wasu ƙarin makarantu a yankin ƙaramar Hukumar Zariya da ke Jihar Kaduna da samar da guraben ayyuka na manyan ma’aikatun Gwamnatin Tarayya.

Abbas Tajuddeen, wanda ya ce shirin da ake yi yanzu na kafa wasu manyan makarantu biyu a Zariyan da aka amince da shi na da nufin magance ƙarancin hanyoyin samar da ilimi da ake da su bisa la’akari da yawan al’umma dake ƙaruwa da kuma ƙarancin guraben karatun musamman manyan makarantu.

Ya kuma ce makarantu ba za a ginasu ba ne kawai don amfanar al’ummar Zaria kaɗai ba daga ko’ina mutum na iya tasowa ya zo domin ya yi karatu a wajen kamar yadda aka san Zariya tuntuni tana da makarantu da ake zuwa karatu daga ko’ina na duniya.

Abbas Tajuddeen wanda ya yi wannan jawabin a wajen taron ƙungiyar bunƙasa ilimi ta lardin Zazzau (ZEDA) da ya gudana a Zariya karo na 31 da 32, mai taken amfanin ilimi ta fannin ƙirƙira da ƙarfafa sana’o’i ga ɗalibai.

A nasa jawabin mai Martaba Sarkin Zazzau Ambasada Malam Ahmad Nuhu Bamalli CFR ya shawarci al’umma ne da su dinga alkinta kayayyakin more rayuwa da gwamnati ke samarwa sannan ya yaba wa kakakin majalisar da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu na amincewa da naɗin daya daga cikin ‘ya’yan da suka fito daga Zariya a matsayin shugaban Kwalejin koyar da tuƙin jirgin sama dake Zariya da wasu manyan muƙamai da aka ba ‘yan Zariyan, sannan sai ya yaba da irin ƙoƙarin da ƙungiyar ZEDA ke yi akan ƙalubalen da fannin ilimi ke fuskanta, sannan ya buƙacesu su fuskanci fannin wayar da kan al’umma musamman iyayen yara da ɗalibai ta yadda za su fahimci irin sauye-sauyen da zamani ya zo da shi ta fannin ilimi da ƙara nuna musu zaɓin da ya dace ta fuskar shiga makarantu da darussan da ɗaliban za su karanta.

Ya kuma ce ZEDA a yanzu wannan shine aikin da za ta tunkara bayan kakakin majalisar ya ɗauke wasu nauye-nauye da suka shafi ƙungiyar da ka iya haifar mata da tarnaki a tafiyar da suke yi.

A jawabin shugaban ƙungiyar Dr Abdul Alimi Bello ya ce wannan taro ya yi armashi ne bayan game tarukan guda biyu da ƙungiyar ta yi wanda ya haɗa da taron na talatin da ɗaya da na talatin da biyu sannan sun shirya tunkarar taronne da zammar yauƙaƙa dangantaka tsakanin makarantu da ake da su a lardin Zazzau don bunƙasa harkar ilimi da samar da kusanci da gabatar da nasarorin da ƙungiyar ta samu tun bayan kafuwar ƙungiyar kimanin shekaru talatin da suka gabata, sannan sun kuma yaba da irin gudunmuwar da suka samu daga kakakin majalisar da neman ƙarin goyon baya na cigaban ƙungiyar ta yadda za ta faɗaɗa ayyukanta kamar yadda aka buƙata.

A ƙarshen taron ƙungiyar ta gabatar da kyaututtuka ga makarantun da suka yi hazaƙa a gasar karatu da ƙungiyar ta shirya don ƙara ƙwazo ga ɗalibai da kuma bada lambobin yabo ga wasu manyan jami’an gwamnati da jagororin al’umma bisa irin rawar da suke takawa na tallafa wa rayuwar al’umma da tsayawa kan buƙatun al’ummar tasu.

By ukarofi