Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
Sabon lauya, Barista Ibrahim Dauda Adamu, wani matashi ne mai ƙarancin shekaru a garin Gombe, wanda ya kasance ya fito daga gidan da ba su da ƙarfi ya ke faɗi-tashin rayuwa, don ganin ya rufa wa kansa asiri. Ibrahim, wanda ya ɗauki sana’ar leburanci ta yin gini a matsayin hanyar dogaro da kai da ita, ya ƙuƙuta ya biya kuɗin makarantarsa daga sakandare zuwa Kwalejin Koyon Aikin Shari’a ta Legal dake garin Yola har zuwa Jami’a, matashin da ya kasance har a jami’a bai bar aikin na leburanci ba, don ya samu kuɗaɗen biyan makaranta yanzu haka ya kammala karatun lauya da sakamako mafi kyau a garin Bwari da ke Babban Birnin Tarayya Abuja, don ji kowane ne Barista Ibrahim, Wakilin Blueprint Manhaja a Gombe, ABUBAKAR A BOLARI, ya samu damar tattaunawa da shi. Masu karatu ku biyo mu;
MANHAJA: Wane ne Ibrahim? Mai karatu zai so jin tarihinka da irin gwagwarmayar da ka yi har ka zama lauya?
IBRAHIM: Sunana Ibrahim Dauda Adamu, an haife ni a unguwar Jekadafari layin Honda ɓilla a cikin fadar Jihar Gombe. A lokacin da na taso a ƙuruciya na yi karatun islamiyya, daga bisani aka sa ni a firamare ta Hassan Central dake Gombe a shekarar 1996 da na kammala firamare sai na tafi sakandare ta Gandu a shekarar 2001 inda anan nayi karama da babbar Sakandare na gama a shekarar 2009 a shekarar da muka kammala Sakandare an soke jarrabawar NECO ta wannan Makarantar gaba daya amma da Allah ya taimakeni na rubuta NECO da WEAC duka a shekarar da aka soke NECO sai ya zama ina da WAEC a wannan lokacin ne na fara tunanin tafiya Makarantar gaba da sakandare wato Jami’a kuma ga kalubalen rayuwa kasancewa ta na fito daga gidan da iyayen sa basu da halin biya masa makaranta wanda nine dan Auta a gidan mu wato nine na 8 a wajen iyayena kuma ‘yayuna ma ba masu karfi bane balle su taimaka min a wannan lokacin na nemi wani aiki sikurity (Security) a ofishin Babayo Goje na wani kamfani mai suna sharp Security Guard ina nema sai Allah ya taimake ni na samu mun fara aikin da wata uku ko wata biyu da kwanaki sai Allah ya yiwa shi mai kamfanin Babayo Goje rasuwa yana rasuwa sai aka tsayar da aikin namu a lokacin sai naji na fara nemi izinin shiga jami’a mallakar jihar Gombe GSU mana sai kuma ya zama banyi JAMB ba, sai aka bani shawarar na tafi Legal ta garin Yola na karanta Law, sai na amince na tafi Yola sai kalubale ya karu na Rashin karfi ga karatu a nesa sai na yanke shawarar bin kan injiniyoyi masu aikin gini ina aikin leburanci na gini da tonon rami ana biya na da haka Allah yasa na tafi Legal Yola a shekarar 2010 na gama a 2012, na samu takardar shaiar Difloma bayan na gama Legal Yola na dawo gida na samu sakamako mafi kyau wato Distinction, a shekarar 2013 nayi tunani tunda na samu sakamako mai kyau na tafi jami’a nayi Digiri mana a wannan shekarar ta 2013 sai na sayi Fom na DE wato direct entry a jam’ar Maiduguri ban samu ba a 2014 na nemi koyarwa a wata makaranta mai zaman kanta dan kar na zauna haka ana biya na dubu bakwai idan na tashi a koyarwa na tafi harkar leburanci, a wannan shekara ta 2014 na sake neman izinin shiga a jami’ar Ahmadu Bello ta Zari’a ABU nan ma ban samu ba duk da haka ina ci gaba da buge-buge na har na fara cire rai da karatu sai naji bai kamata na hakura ba tunda ina da burin da nake son na cika a rayuwa ta a shekarar 2015 sai na sake neman jami’ar Bayero ta Kano inda wani Malami dan Gombe a jami’ar dan gidan marigayi Zannan Gombe Alhaji Saleh Kilawa Mai suna Habibu ya taimaka min na samu adimision wani abun takaici sai aka ce an janye izinin shigar saboda Kwalejin shari’a ta Legal Yola da na yi sun samu matsala da jami’ar Bayero domin ita tana da rijista ne da ABU Zari’a ne na sake shiga gwagwarmaya a shekarar 2016 na sake neman izinin shiga a jami’ar Jos inda an je aka tantance ni ina jiran admission da aka fitar ban samu ba anan ne na yanke hukunci cewa na hakura da karatun gaba daya gara naci gaba da buge-buge da leburanci na yafi min, a 2017 ina magana da wani sai yake ce min ai an gyara matsalar da ke tsakanin jami’ar Bayero da legal ta Yola za su iya bani admission sai banyi kasa a guiwa ba na sake nema kuwa suka sake bani to kaji gwagwarmayar da nayi har na samu shiga jami’a a shekarar 2017 inda na shekara shida saboda annobar Korona da yajin aiki, da an shiga yajn aiki sai na tattara na koma wajen leburanci kafin a dawo karatu wanda har a wasu sassan gine-gine na jami’ar Bayero din akwai inda dani aka gina ina matsayin Lebura, Randa ba leburanci ina karbar typing din dalibai ina hana idona bacci ina buga musu a kwamfuta har asuba dan na samu yan kudaden da zan biyawa kai na bukata anan ne wani abokin kwana na a dakin mu wani dan garin Suleja a jihar Neja yake ce min na rage wasu abubuwan kar na takura kai na na jefa kaina cikin wata damuwa inda yake ce min in dinga daukar rayuwa da sauki
Ka ce har a cikin jami’ar ka yi leburanci, kana ɗalibi ne kake leburancin ko ya abun yake?
ƙwarai da gaske a tsohon sashin jami’ar wato old side na Bayero a ɓangaren ɗakin gwaje-gwaje Industrial Chemistry Laboratory wajen da aka yi wa kwaskwarima da wani kamfani mai suna Nakowa Nigeria Construction Limited ya gina nayi aikin leburanci da su a wajen, haka ma a ƙofar mai Martaba Sarkin Kano akwai gine-gine da aka yi a wajen nan ma akwai waɗanda na yi leburanci gini a wajen, bayan nan akwai wurare da dama a cikin Kano da na yi leburanci ina ɗalibin jami’a, da haka na yi ta faɗi tashi har na kammala jami’a a shekarar 2023 na gama kuma da sakamako mai daraja ta biyu wanda nine na biyu a ɓangaren shari’a da ya samu sakamako mafi kyau second class upper. Bayan mun gama aka zo aka ce za mu tafi makarantar lauyoyi law school anan ne wani sabon babi na kalubale ya sake budewa domin bani da kudi kuma an kara kudin makarantar da a da ake biyan naira dubu dari biyu da casa’in da shida daga kan mu ya koma dubu dari hudu da saba’in da shiga da haka da kyar da fadi tashi na samu na tafi nayi rijista can ma muka shekara daya muka gama amma a can banyi leburanci ba saboda a tsarin su ko ma’aikacin gwamnati ne kafin su baka admission sai ma’aikatar ku ta tura musu takardar cewa an baka izini kayi karau saboda ba yadda za a yi kana cikin karatu ka bari ka koma wajen aiki, to tunda acan ba damar yin leburanci amma ana bayar da ayyuka wato assignment anan ne naci gaba da karba ina bugawa mutane a kwamfuta ina samun taro da kobo, na shiga makarantar a ranar 29 ga watan Janairu mun gama ranar 9 ga watan Nuwamba 2015 nan ma na gama da sakamako mai Daraja ta biyu second class upper.
Wane irin gudunmawa iyaye suka bayar duk da halin ƙunci na rashi da ba su da shi?
Kasan iyaye duk da ba su da shi wani lokacin ma nine idan zan tafi nakan ɗauki wani abu daga kuɗin da na samu na basu amma suma wata rana mahaifiya ta takan ba ni dubu biyu mahaifina ya bani dubu uku da haka suna min albakar har na je na dawo.
Yayyenka fa akwai wata rawa da suka taka wajen tallafawa?
Eh akwai duk da dai da gaske talakawan ne amma sun yi ta iya nasu ƙoƙarin domin akwai ranar da zan koma ba ni da kuɗi ɗaya daga cikin yayun nawa ya kama akuyarsa da yake kiwo ya sayar ko naira bai ɗauka a cikin kuɗin ba ya ban kuɗin duka ya ce na yi kuɗin mota na riƙe sauran
Yanzu ka kammala karatu ka zama cikakken Lauya ya batun buɗe Chamber ka fara zuwa kotu?
Gaskiya buɗe Chamber ba abu ne mai sauƙi ba, domin akwai buƙatar kuɗaɗe na kama hayar ofis da kuma sayen littatafi na yau da kullum wanda ma dai ba lailai sai a lokaci daya za ka saye su ba amma dai kudin suna da yawa ga kuma rijista da za kayi da C.A.C da sauran su amma dai zan duba yiwuwar zama a karkashin wani na fara koyon aiki kafin na samu yadda zanyi
Mene ne shawararka ga matasa ‘yan uwanka na ganin sun jajirce don zama masu ƙwazo kar rashin kuɗi ko tallafi ya kashe musu guiwa kamar yadda ka yi faɗi tashi har ka cimma burinka?
Shawarata ga matasa anan shi ne kamar yadda ake faɗin cewa himma ba ta ga rago to gaskiya su tashi su jajirce domin dan ganin ka tashi kaga gidan ku talakawa ne kar ka yi ƙasa a guiwa ka tashi ka zama cewa za ka iya canja wannan yanayi ku zama gidan da yafi kowa, kamar misalin da Grand Khadi Abdullahi Maikano Usman, yake ban shawari na cewa duk da damar da ka samu a rayuwa ka taimaki wani kar kaji gyashin taimakawa wani sai dai kuma za ka iya ganin matashi da wayar sama da dubu dari uku da babur mai tsada amma zai iya ce ma bai samu damar yin karatu ba saboda Rashin kudi, akwai lokacin da ina jami’ar ma bani da babbar waya kai akwai lokacin da na sheakar biyu bani da waya idan zan buga waya da wayar abokin kwana na nake waya a gidan mu idan za’a neme ni ma ta wayar sa ake nema ba saboda bani da waya kuma ka duba karatu irin na jami’a akwai shiga yanar gizo dan yin nazari da sauran su amma da haka nayi karatun domin masu Karin Magana sun ce idan kace sai ka samu dama za ka yi abu to ba zaka samu damar ba idan damar tazo komai kadan din ta ka samu kayi amfani da ita ka hada da gwagwarma sai kayi nasara
Daga ƙarshe mene ne fatar ka?
To ni dai fatana shi ne naga na samu aiki da daukakar da zan iya alfahari da ita wajen taimakawa iyaye na da sauran yan uwana naga na taimaka musu sunyi karatu bana fata wani dan uwana ya sha wahalar karatu irin wacce na sha a baya
Akwai iyalai ne idan akwai ya aka haɗa wannan gwagwarmayar karatun da kuma riƙe gida?
Batun iyali wani abun al’ajabi ne domin an min aure ba tare da na kashe ko naira daya ba kuma auren anyi shi ne a lokacin da nake makarantar Lauyoyi, Yarinyar Yar Bappah na ce an daura mata aure da wani bayan an daura auren aka samu tangarda tsakanin iyayen Yaron da ita Yarinyar da tasa ko tarewa ba tayi ba aka raba aure su sai Bappah na yace a daura min aure da ita duk da yasan halin da nake ciki na Rashin kudi ga gwagwarmayar karatu, wanda yan uwa ne suka yi karo karo suka hada kudi suka min auren wani ya bada gidan da zamu zauna har na dawo idan na gama karatu na samu inda zan zauna sannan na fita, wani ikon Allah kuma an daura auren da wata biyu banga matar ba har sanda na gama karatu na dawo kuma yanzu haka muna tare da yake ‘yar uwa ta ce ba wani matsala.
