Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani ɗan Nijeriya mai suna Olabode Ifeanyi ya sake sayen dukkan kayayyakin da ya saya a wani shagon sayar da kayan abinci a shekarar 2020 domin auna yadda farashi ya canja, inda ya gano cewa kuɗin kayan sun tashi da kashi 582 cikin shekara shida.
Ifeanyi ya wallafa labarin a shafinsa na ɗ, inda ya ce ya yanke shawarar gwada sayen dukkan kayayyakin da ke jikin rasitin sayayyarsa ta 2020 domin auna tasirin hauhawar farashi a tsawon lokaci.
Daga bayanan rasit ɗin da ya wallafa, kuɗin dukkan kayayyakin da ya saya a 2020 ya kai naira 25,225. Amma lokacin da ya koma sayen irin waɗannan kayayyaki a watan Janairun 2026, jimillar kuɗin ya haura zuwa naira 147,050.
Idan aka duba bambancin kuɗin, hakan na nuna ƙaruwar farashi da kusan kashi 582 cikin ɗari a cikin shekara shida kacal.
A cewarsa, “Idan albashinka bai ninka sau shida ba tun daga 2020 zuwa yanzu, to a zahiri kai talaka ne a yau.”
Rasit ɗin sun nuna cewa kayayyakin da ya saya iri ɗaya ne a shekarun biyu, ciki har da kayan abinci, abubuwan sha, kayan tsafta da sauran kayayyakin gida.
Ifeanyi ya ɗora alhakin wannan hauhawar farashi kan halin tattalin arziki da gwamnatin jam’iyyar APC ke tafiyarwa, yana mai sukar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Ya ce, “APC ta lalata tattalin arzikin ƙasa, kuma Tinubu yana daf da kammala abin da ya rage.”
A halin yanzu Nijeriya na fama da tsananin matsin tattalin arziki, inda hauhawar farashi ta kai ƙololuwa musamman kan kayan abinci. A wani lokaci, an ce hauhawar farashi ta kai kashi 40.9 cikin ɗari, kodayake ta ragu zuwa kashi 15.15 a watan Disambar 2025. Duk da haka, al’ummar ƙasa da dama na ci gaba da kokawa wajen samun kayan masarufi na yau da kullum.
