Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranci tawagar Nijeriya zuwa taron shekara-shekara na Dandalin Tattalin Arziki na Duniya (World Economic Forum) karo na 56 da ake gudanarwa a Davos, ƙasar Switzerland.
Rahotanni sun bayyana cewa taron zai gudana daga ranar 19 zuwa 23 ga watan Janairu, 2026, inda shugabannin gwamnatoci, manyan ’yan kasuwa, jagororin ƙungiyoyin farar hula da kuma ’yan jarida daga sassa daban-daban na duniya za su hallara.
Zuwan Mataimakin Shugaban ƙasar zuwa Switzerland ya biyo bayan ziyararsa zuwa Conakry, ƙasar Guinea, inda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a bikin rantsar da Shugaban ƙasar Guinea, Mamadi Doumbouya, a ranar Juma’a.
A cewar wata sanarwa daga Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwa ga Mataimakin Shugaban ƙasa, an tarbi Shettima a filin jirgin sama da Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dr Jumoke Oduwole, da jami’an ofishin jakadancin Nijeriya a Switzerland.
Taron na shekara-shekara na Davos na jan hankalin dubban mahalarta, ciki har da shugabannin ƙasashe, manyan daraktocin kamfanoni, ‘yan fafutuka da masu ruwa da tsaki a fannoni daban-daban.
Ana sa ran taron bana zai mayar da hankali kan ƙƙlubalen tattalin arzikin duniya, ƙirƙire-ƙirƙiren fasaha da kuma matakan kare muhalli daga sauyin yanayi.
Shekarar 2026 ta zo da wani sabon salo a halartar Nijeriya taron, inda gwamnatin tarayya ta kafa rumfar ƙasa ta musamman a karon farko a titin Davos Promenade. An sanya wa rumfar suna “Nigeria House Davos,” kuma an kafa ta ne ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu.
Za a yi amfani da rumfar a matsayin cibiyar ganawa da ministoci, tattaunawar zuba jari da kuma gabatar da al’adun Nijeriya a tsawon makon taron. Ana sa ran Mataimakin Shugaban ƙasa zai ƙaddamar da rumfar a yayin ziyararsa.
Yayin da take magana da ‘yan jarida bayan isowar Shettima, Minista Oduwole ta ce Nijeriya za ta gabatar da tsare-tsaren zuba jari masu ƙarfi a lokacin ƙaddamar da Nigeria House. Ta ce za su baje kolin manyan tsare-tsare huɗu na Shugaba Tinubu wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.
“Za mu gabatar da ɓangaren ma’adinai, ɗorewar muhalli, noma da kuma ɓangaren ƙirƙira da fasahar zamani ga masu zuba jari daga sassa daban-daban na duniya,” inji ta.
A nata ɓangaren, mai ba da shawara kan harkokin yaɗa labarai ga Mataimakin Shugaban ƙasa, Nkwocha, ta bayyana cewa Shettima zai gabatar da hangen nesa na tattalin arzikin Nijeriya na shekarar 2026 ga shugabannin duniya a yayin taron.
Haka kuma zai halarci manyan zaman tattaunawa da za su mayar da hankali kan amfani da fasahar zamani kamar ƙirƙirarriyar Basira ta AI, ƙuantum computing da kuma ilimin halittu (biotechnology) cikin hikima.
Ana kuma sa ran Mataimakin Shugaban ƙasa zai gudanar da ganawar ƙashin kai da shugabannin ƙasashe, manyan jami’an kamfanonin duniya da kuma shugabannin cibiyoyin tallafin raya ƙasa a tsawon makon taron.
