Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Ƙungiyar tattaunawa da muhawara ta ƙasar ƙasa wato DEEDS Dialogue debate international ta shirya muhawara tsakanin Farfesa Ibrahim Bello Kano da Dr. Bala Muhammad na Jami’ar Bayero, Kano.
Taken tattaunawar shi ne: Tsakanin littafi da Allon zamani shin fasahar zamani ta kashe son karanta Littafi”?
wato BOOK vs Screens: Has the digital age killed the love for Reading?
Taron ya gudana a ɗakin taro na Jami’ar Khalifa Isyaka Rabi’u, KHAIRUN Kano.
Tun da farko a jawabinsa Malam. Khalil Imam wanda shi ne shugaban ƙungiyar na ƙasa ta DEEDS wato Dialogue debate International ya bayyana cewa manufar shirya taron shi ne samar da zauren tattaunawa na ilimi da zai dauke hankalin matasa su samu abinda zai ilmantar da su.
“Idan ka lura yanzu musamman a kafafen sada zumunta ya zama kowane shirme ya zama shi ne ilimi mu rungume hannunmu ba mu yi wani abu ba waye zai yi mana, to sai muka ga cewa ya kamata mu samar da wani zaure wanda za’a samu gogaggun masana da suka ƙware a fannin ilimi ko aiki ya zo mu gabatar da shi a matasa cewa wannan da kuke gani ya yi karatu, shi yasa ya kai wannan matsayi, sannan kuma Ilimin da zai bayyana ya amfanar da su”
Alhamdulillah wanda duk ya zo gurin taron nan zai ga cewa matasa sun cika ɗakin taron nan abinda muke buƙata mun cimma sa”.
Shi ma da ya ke nasa jawabin, Shugaban Jami’ar KHAIRUN, Farfesa Abdurrashid Garba, ya bayyana cewa, ɗimbin amfani na ilimi da al’umma suka samu ya sa suka baiwa wannan ƙungiya ɗakin taro da duk abinda za ta taimaka taron yin nasara.
Ya ƙara da cewa ” an zo an baza mana ilimi akan maɓubbugar ilimi wacce ta fi inganci mu ɗora ga ilimi kamar yadda kakanni mu suka fara ko mu ɗora da zamani ta yadda kowa ya ke tafe da ilimin a wayarsa, a fahimta ta ka riƙe duk biyun, duk inda ya kama ka yi saboda ba’a raina maɓubbugar ilimi ta inda ba ka zato ta nan zaka sami ilimin da zai amfane ka a duniya da lahira” inji Farfesa Abdurrashid
Muhawarar wacce Farfesa Abdullah Uba Adamu ya kula da ita ta samu halartar masana daga makarantu da dama da kuma ɗimbin matasa maza da mata.
