Daga HASSAN IMRAN
Masana na cewa, ‘Aure ibada ne, saboda haka zamantakewar aure tana buƙatar a ƙarfafa danƙon so da ƙauna a zukatan ma’aurata ta hanyar kyakkyawar kulawa da juna wacce za ta haifar da zaman lafiya da natsuwa zuciya.’
A wasu shekarun baya, haka iyayenmu da kakaninmu suka kyautata zamantakewar aurensu wacce a sanadiyyar haka aka samu ‘ya’ya masu albarka waɗanda al’umma ke alfahari da su. Mata a wancan zamani sun kasance masu biyayya ga mazajensu kuma suna bada kulawa sosai a harkokinsu na gida. Waɗannan mata suna da himma da jajircewa wajen tarbiyyantar da ‘ya’yansu bisa turba tagari wanda a sanadiyyar haka aka samu ingantacciyar al’umma.
Abin takaici da mamaki shi ne yadda zamantakewar auren a wannan zamani da muke ciki ta munana; da yawa daga cikin samari na aure ne domin samun abin duniya ma’ana auren jari, wasu na aure ne domin magance sha’awar su, wasu kuma na aure ne domin gasa da abokansu waɗanda suka riga su aure. Wasu kuma na aure ne ba tare da suna da wani ƙwaƙƙwaran aiki ko sana’a ba, wacce za ta sauƙaƙa masu ɗawainiyar kulawa da iyali. Bugu da ƙari, da yawa daga cikin samari na neman aure ne ba tare da sanin ladubobi da kuma hukunce-hukuncen auren, da kuma sanin yaya ake zamantakewar aure ba. Wannan shi ke haddasa yawan matsalolin aure a Arewa. Za ka ga an yi bikin aure bayan wasu satittika ko ‘yan watanni, aure ya rabu, saboda wata ƙaramar matsala da ta faru tsakanin ma’auratan. Wannan shi ya sa saki ya yawaita a cikin al’ummarmu. Yawan auri – saki da ake samu a mafi akasarin jihohin Arewa, musamman a tsakanin Hausawa, ya zama wata matsala da take ci mana tuwo a ƙwarya a Arewacin Nijeriya. Dole a nemi ƙwararan matakai domin magance wannan matsalar.
A ƙasar Sudan suna da wani tsarin a kowanne masallaci akwai kwamiti na masana akan lamurran aure wanda aikinsu shi ne horar da samari da budurwa a duk lokacin da suka shirya yin aure. A kowanne masallaci akan horar da su a wurin da ake ɗaura musu aure. Sa’annan za a basu takardar shaidar aure a yayin da suma za su ajiye irin takardar a hannunsu, domin masu shaida. Idan wata matsalar aure ta taso a tsakanin ma’aurata, za su garzaya zuwa masallacin ne domin neman shawararsu akan abinda ya faru. Idan al’amarin ya yi muni kuma zamantakewa ta gagara yin daɗi, za su bashi shawarar ya saki matarsa, bayan ya rubuta wa kwamitin wasiƙa da dalilansa na yin saki ko neman saki. Sai su kwamitin sun rattaɓa hannu a kan wasikar sa, sannan za a ba su damar rabuwa. Ashe idan da za mu yi koyi da wannan tsarin za a samu rage yawan auri-saki da ake yi.
A wasu makonni da suka gabata, tashar BBC Hausa ta rawaito wani labari mai cike da tausayi da ban haushi, inda aka bayyana cewa wani saurayi a Jihar Jigawa ya auri wata mata sun kwana biyu babu wata alaƙar da ta shiga tsakaninsu. Ya yi iya ƙoƙarinsa domin ya samu damar kwanciyar sunna da matarsa, amma ta ƙi. Da ya kasa jurewa akan lamari maimakon ya nemi wata hanyar shawo kan wannan matsala sai ya gayyaci abokansa guda uku suka zo gidansa suka danne masa matar har ya yi saduwar aure da ita, ƙarfi da ya ji. Wannan al’amari shi ya yi ajalinta. Yanzu wannan hauka da rashin ilimi da mai ya yi kama?
Haka zalika, akwai wani labarin da ya janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta wanda har wasu malamai suka yi bayanai da nasihohi akai. Labarin ya faru ne a Kano yayin da wata mata ta saka wa mijinta guba a abinci, da ta ga wannan gubar bad kashe shi yadda take so ba sai ta yi wa mijin yankan rago. Wannan mugunta da rashin imani da mai ya yi kama?
Ire-iren waɗannan labarai da suke bakantawa mutane rai suna nan da yawa, kuma akasari abubuwan na faruwa ne a garuruwa da jihohin Arewa.
Akwai dalilai da daban-daban suke janyo waɗannan matsaloli a zamantakewa aure; daga ciki akwai auren dole da wasu iyaye ke wa ‘ya’yansu, domin wani abin duniya ko wani dalilin na daban da ba shi da wata alaƙa da addini. Sa’annan akwai rashin wayarwa matasa kai akan haƙƙoƙin mata da miji a musulunci. Matasa in sun tashi aure sun fi damuwa da dawainiyar da kuma shirye-shiryen harkokin bikin aure ba tare da mayar da hankali akan zamantakewar aure da Musulunci ya koyar ba. Galibi ma, akwai wasu al’adu marasa inganci da ake yi a gabani da kuma lokutan bukukuwan aure, irinsu hotunan da basu dace ba, wanda a turance ake kiransu pre-wedding pictures da wasu al’adu irin su ‘ƙauyawa Day,’ da cakuɗewar maza da mata a wajen liyafar biki da sauran al’adun turawa da aka shigo da su cikin bukukuwan aure.
Har wayau daga cikin matsalolin zamantakewa aure, akwai rashin ƙwararan binciken akan halayen ma’auratan da kuma rashin gwaje-gwajen cututtukan zamani irinsu gwajin jini da lafiyar ƙwaƙwalwa da sauran su. Haka zalika, rashin sana’a ko kuwa ƙwaƙƙwaran aikin da zai tallafawa saurayi wajen kula da iyalinsa, duk waɗannan na iya haddasa matsaloli bayan aure. Sa’anan akwai ƙarancin tattaunawa da kuma rashin fahimtar juna tsakanin ma’aurata, da rashin tarbiyyar wasu matan, duk hargiza zamantakewar aure.
Yana da kyau iyaye su yi koyi da sunnar Manzon Allah; game da yadda ya kasance yana kulawa da al’amarin ‘yarsa Nana Faɗimatu bayan aurenta da Sayyidina Ali. Yana kai mata ziyara har gidanta, kuma yayin da wata matsala ta taso yana taimaka wa masu wajen sasanta su ba tare da son kai ko kuwa raba aurensu ba. Da yawa akwai wasu iyayenmu da zarar sun aurar da ‘ya’yansu shi kenan sun fita batun ta kuma babu wata bibiyar ta ko kuma nuna damuwa akan al’amurinsu. Wannan shi ke sa wasu mazan marasa tausayi suke gallazawa mata suna cin karensu babu babbaka.
Malamai suna da haƙƙin ilimantar da mabiyansu akan haƙƙoƙin ma’aurata a musulunci. Sa’annan hukumomi irin su Hizba da kuma wasu ƙungiyoyi na addini ya kamata a buɗe makarantu ko cibiyoyi na musamman, ko kuma kawo wani shiri na musamman, domin ilimantarwa da kuma wayarwa ma’aurata kawunansu, game da koyarwar addinin Musulunci akan zamantakewar aure. Iyaye su zurfafa bincike akan halayen matasan, maza da mata, kafin shirya bikin aure. Iyaye su kiyaye auren dole domin ya saɓawa karantarwa Musulunci da kuma ilimin zamani. Iyaye suna bada kulawa ga ‘ya’yansu bayan aure ba tare da shi shige masu ba, ta hanyar da bata dace ba. Gwamnati ta ɗauki ƙwararan matakai a kan al’amarin aure a Arewacin Nijeriya ta hanyar sauƙaƙa wa mutane tattalin arziƙi wacce zai kawo sauƙin rayuwa.
Allah Ya kawo mana sauƙin rayuwa ya kuma sauƙaƙa wa ma’aurata zamantakewar aure a tsakanin su. Allah Ya kawar da duk wasu fitintinu da kuma rikice-rikice da suke haifar da matsalolin zamantakewa aure a ƙasar mu. Amin.
Hassan Imran ya aiko da wannan nasiha ne daga Jos, kuma za a iya samun sa kan addreshinsa na yanar gizo: [email protected]
