
Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana irin rawar da Shugaba Bola Tinubu ya taka wajen daƙile yunƙurin juyin mulkin da aka yi ranar Lahadi a Jamhuriyar Benin da ke maƙotaka da Nijeriya.
Wata sanarwa daga Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, fadar ta ce shugaba Tinubu ya tura sojojin sama da na ƙasa zuwa Benin bisa buƙatar da gwamnatin ƙasar ta gabatar.
Da safiyar lahadi ne tawagar wasu sojoji ƙarƙashin Laftanar Kanar Pascal Tigri ta sanar da kifar da gwamnatin shugaba Patrice Talon a kafar talabijin ta ƙasar.
Saidai da rana, ministan harkokin cikin gida na Jamhuriyar Benin Alassane Seidou ya bayyana a gidan talabijin ɗin ƙasar, inda ya sanar da cewa yunƙurin juyin mulkin da wasu sojoji suka yi bai yi nasara ba.
Haka nan bayan shafe yini ba tare da an ji ɗuriyar shugaban ƙasar ba, daga baya Patrice Talon ya bayyana a kafar talabijin inda ya yi wa al’ummar ƙasar jawabi, tare da bayyana cewa an daƙile yunƙurin juyin mulki da wasu sojoji suka yi a ƙasar, kamar yadda BBC Hausa taruwaito.
Ya ce, “yanzu an shawo kan lamarin baki ɗaya” bayan yunƙurin da masu juyin mulki suka yi tun da farko.
Ya zuwa yammaci mazauna Cotonou, babban birnin ƙasar ta Benin sun bayar da rahoton jin ƙaran harbe-harbe da fashewar wasu abubuwa.
Rahotanni sun ce an kyautata zaton cewa fashewar ta samo asali ne daga wasu hare-hare ta sama.
