
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An samu aukuwar wani al’amari mai kama da wasan kwaikwayo yayin taron bikin Ooni na Masarautar Ife karo na 10 a Jihar Osun yayin da matar Shugaban Ƙasa Sanata Remi Tinubu ta ari numfashin Gwamna Ademola Adeleke a lokacin da yake tsaka da jawabi.
Taron, wanda aka gudanar a ranar Lahadi, ya yi daidai da cikar Oba Adeyeye Ogunwusi shekaru 10 akan kujerar sarautar.
A yayin haka ne kuma Sarkin ya ba wa matar shugaban ƙasar sarautar ‘Yeye Asiwaju Oodua’ na masarautar.
Haka kuma taron ya samu halartar manyan baƙi daga sassa Nijeriya ciki har da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’a Abubakar da tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo da Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas da Dapo Abiodun na Jihar Ogun.
Sauran mahalartan sun haɗa da Jagora a Majalisar Dattawa Opeyemi Bamidele, tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Oladimje Bankole, tsohon gwamnan Ogun Ibikunle Amosun da matar tsohon shugaban ƙasa Dakta Patience Jonathan da kuma matar mataimakin shugaban ƙasa Hajia Nana Shettima da dai sauransu.
Kamar yadda wani faifan bidiyo ya nuna, an ga yadda Gwamna Adeleke yake jawabi cikin nishaɗi ga magoya bayansa, lamarin da matar shugaban ƙasar ta nuna rashin gamsuwa a kai, inda ta je ta same shi ta ce masa ya mayar da hankali akan tsokacinsa ba “ɓata lokaci ba”.
Wannan al’amari ya tayar da hazo musamman a kafafen sadarwa inda al’umma da dama suka yi ta nuna mamaki a kai musamman bisa la’akari da matsayinta a Nijeriya.
