Yadda tsoron saki da abin da mutane za su ce ke tura wasu mata mahalaka

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Akwai wata kalma da kusan kowace mace mai aure ta taɓa ji a rayuwarta, musamman a lokacin da wani abu ya rikice a tsakaninta da mijinta: “Ki yi haƙuri.” Wataƙila mahaifiyarta ce ta faɗa mata, ko ƙawarta, ko wata dattijuwa da take ganin ta fi ta sanin rayuwar aure. Wataƙila ma malami ne ya ce mata haka. Kuma a mafi yawan lokuta, ba a faɗi kalmar da mugun nufi ba. Ana faɗarta ne saboda an san cewa aure yana buƙatar haƙuri, domin babu gidan da yake tafiya ba tare da kuskure, sabani da lokutan da ake buƙatar a danne fushi domin a ceci abin da aka gina ba. Amma idan muka tsaya muka kalli kalmar sosai, sai mu ga cewa akwai wani bambanci mai girma tsakanin haƙurin da ake yi domin a gyara abin da ya samu matsala da kuma haƙurin da ake buƙatar mace ta yi domin a ci gaba da barin abin da ke cutar da ita.

Haƙuri a Musulunci ba ƙaramin abu ba ne. Yana daga cikin siffofin da aka ɗaukaka, kuma rayuwar mumini kanta tana buƙatar haƙuri a lokuta daban-daban. Aure ma ba zai iya ɗorewa ba tare da shi ba. Miji zai yi kuskure, mace za ta yi kuskure; wani lokaci za a yi magana cikin fushi, wani lokaci a samu rashin fahimta, wani lokaci kuma matsin rayuwa ya sa ɗaya daga cikin ma’auratan ya kasa nuna halin da ya saba da shi. A irin waɗannan lokutan, haƙuri na iya zama abin da zai hana ƙaramin abu ya zama babban rikici. Ya sa a dakata kafin a yanke hukunci, a saurari juna, a ba da dama ga gyara, a nemi sulhu, a tuna da abubuwan alherin da suka haɗa mutane biyu tun farko. Wannan shi ne irin haƙurin da ke taimaka wa aure.

Amma aure da Musulunci ya gina ba a kan haƙuri kaɗai yake tsaye ba. Akwai soyayya, rahama, natsuwa, kyautatawa da kiyaye hakkokin juna. Shi ya sa ba za a ɗauki kalmar haƙuri a ware ta daga sauran abubuwan da Shari’a ta tanada a cikin zamantakewar aure ba. Miji yana da hakkoki a kan matarsa, amma yana da nauyin da Allah Ya ɗora masa a kanta. Mace tana da nauyin da ya rataya a wuyanta, amma ita ma tana da hakkoki da mutuncin da ba a halicce ta aka yi watsi da su ba. Biyayya ba ta nufin a mayar da mace marar hakki, kamar yadda kasancewar mutum miji ba ya ba shi izinin yin abin da ya ga dama ga matar da take ƙarƙashin amana da kulawarsa.

A nan ne matsalar take fara rikitarwa. Domin a wasu lokuta, mace ba ta zuwa neman saki; tana zuwa ne neman wanda zai taimaka mata. Ta yi kuka saboda mijinta ya wulƙanta ta, sai a ce mata ta yi haƙuri. Ta sake dawowa bayan an maimaita abin, sai a sake ce mata ta yi haƙuri. Ta ce tana tsoron mijinta, ko tana fama da cin zarafi, ko rayuwarta ta zama cike da kuka da tsoro, sai a ce mata “aure kenan.” A hankali, kalmar da aka fara amfani da ita domin ƙarfafa ta sai ta zama wata hanya ta rufe abin da ke faruwa. Ba a ƙara tambayar abin da ya sa take kuka; abin da ake nema kawai shi ne ta koma ta ci gaba da zama.

Amma idan aka ce mace ta yi haƙuri, menene ake son ta yi haƙurin a kai?

Idan matsala ce da za a iya gyarawa, a gyara ta. Idan rashin fahimta ce, a zauna a fahimci juna. Idan miji ya yi kuskure, a yi masa nasiha, a nemi ya gyara. Idan mace ta yi kuskure, ita ma a taimaka mata ta gane ta gyara. Idan rikici ya yi tsanani, a shiga tsakanin ma’auratan da hikima domin a yi ƙoƙarin sasanta su. Amma idan abin da ke faruwa shi ne ci gaba da cin mutunci, duka, tsoratarwa, wulƙanci ko wata cutarwa da take jefa mace cikin haɗari, to bai kamata a ɗauki “ki yi haƙuri” a matsayin mafita ta ƙarshe ba. Domin haƙurin da ba ya tare da ƙoƙarin dakatar da zalunci zai iya zama hanyar da ake tsawaita wahala ne, ba hanyar da ake gyara aure ba.

Wannan shi ne abin da ya kamata mu sake fahimta game da auren kansa. Aure ba wurin da ake buƙatar mutum ya rasa kansa domin ya tabbatar da cewa ya iya zama da wani ba ne. A Musulunci, an gina aure ne domin samun natsuwa, soyayya da rahama. Idan aka samu matsala, ba a ce a rufe ido kawai ba; an tanadi hanyoyin gyara, nasiha da sulhu. Idan aka samu saɓani mai tsanani, akwai umarnin neman masu sulhu daga ɓangarorin biyu. Ma’ana, Shari’a ba ta ce kawai “ku zauna komai abin da yake faruwa” ba. Ta kuma damu da yadda za a magance abin da ya shiga tsakanin ma’auratan.

Saboda haka, idan mace ta daɗe tana kuka a gidan aure, abin da ya kamata ya fara damunmu ba wai kawai yadda za mu hana ta neman saki ba ne. Ya kamata mu fara tambayar kanmu abin da yake sa take tunanin saki tun farko. Me ya faru da gidan da ya kamata ya zama wurin natsuwarta har ta fara kallon fita a matsayin mafita? Me ya sa ta kai ga jin cewa komawa gidan iyaye ya fi zama a gidan mijin? Kuma me ya sa wasu mata, duk da irin wahalar da suke ciki, suke ci gaba da zama?

Amsar tana da alaƙa da abubuwa da yawa, amma ɗaya daga cikin mafi girman nauyin da ke riƙe wasu matan a irin wannan yanayi shi ne tsoron saki da abin da mutane za su ce.

Domin ga mace mai aure, saki ba wai kalma ce kawai da take nufin ƙarshen zamantakewa da mijinta ba. A wasu al’ummomi, musamman inda ake ɗaukar aure a matsayin ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke tabbatar da martabar mace a idon jama’a, saki yana zuwa da wasu tambayoyi da yawa. Ina za ta koma? Wa zai karɓe ta? Me za a ce game da ita? Yaya za ta reni ’ya’yanta? Za a zarge ta ne ko a zargi mijinta? Iyayenta za su ji kunya? Dangin mijinta za su yaɗa magana? Makwabta fa? Abokai fa? Kuma bayan duk wannan, za ta iya fara wata sabuwar rayuwa kuwa?

Wannan shi ne dalilin da ya sa wani lokaci mace take zama a gidan da ba ta farin ciki a ciki, ba don tana ganin abin da take ciki ya dace ba, amma saboda abin da take tsoron zai biyo bayan barin gidan.

Wataƙila tana da yara ƙanana da ba ta san yadda za ta kula da su ita kaɗai ba. Wataƙila ba ta da sana’a ko abin da take samu na kanta. Wataƙila iyayenta ba su da ƙarfin da za su iya ɗaukar nauyinta da ’ya’yanta. Wataƙila ma iyayen suna raye, amma tun farko sun riga sun gaya mata cewa “duk abin da ya faru, kar ki dawo.” Wataƙila ta san cewa idan ta koma, za a dinga kallonta da idon matar da ta kasa zaman aure. Don haka sai ta koma wurin da take wahala, ba saboda ta manta da abin da yake faruwa ba, sai saboda ta kasa ganin inda za ta dosa idan ta fita.

A irin wannan yanayi, mace na iya zama cikin aure tana fama da abu biyu a lokaci guda: abin da ke faruwa a gidan da kuma tsoron abin da zai faru idan ta bar gidan. Kuma wani lokaci wannan na biyu shi ne ya fi ɗaure ta.

Wannan ne ya sa ba za mu iya kallon shiru a matsayin alamar cewa mace ta yarda da abin da ake yi mata ba. Akwai mace da take shiru saboda tana jin tsoro. Akwai wadda take shiru saboda ba ta san wanda za ta faɗa wa ba. Akwai wadda take shiru saboda duk wanda ta faɗa wa yana gaya mata ta koma ta yi haƙuri. Akwai wadda take shiru saboda ta san cewa idan ta yi magana, abin da zai fara yawo ba labarin abin da ta sha ba ne, sai labarin cewa “ta kasa zaman aure.”

Wannan nauyin yana da hatsari saboda yana iya sa mace ta fara ɗaukar wahalar da take ciki a matsayin farashin da dole ta biya domin ta ci gaba da samun sunan matar aure. Ta iya kai wani matsayi da ba ta ƙara tambayar kanta ko tana cikin farin ciki ba; abin da take tambaya shi ne ko za ta iya ci gaba da jurewa. Ta kan daina neman mafita, ta fara neman ƙarfin da za ta ci gaba da ɗaukar abin.

Kuma a nan ne ya kamata mu sake duba yadda muke tarbiyyar ’ya’yanmu mata.

Akwai muhimmiyar daraja a koya wa yarinya cewa aure yana buƙatar haƙuri, ladabi, biyayya da kula da gida. Amma idan muka koya mata waɗannan abubuwa ba tare da koya mata cewa tana da mutunci, tana da hakkoki, kuma tana da damar neman taimako idan aka zalunce ta ba, to muna iya gina mata fahimta guda ɗaya ce kawai: komai ya faru, dole ki zauna. Wannan ba shi ne cikakken ilimin aure ba. Kuma sakamakon shi zai iya zama wanda za a yi danasi.

Haka ma ba za a gyara matsalar aure ta hanyar koyar da mata yadda za su jure kawai ba. Dole ne a koya wa samari tun kafin su yi aure cewa zama miji ba wai samun wanda zai yi masa biyayya ba ne kawai. Nauyi ne. Amana ce. Kulawa ce. Mutunci ne. Namiji da yake son a girmama shi a matsayin miji ya kamata ya fahimci cewa shi ma yana da abin da zai amsa a kai. Annabi rahman (S.A.W) ya yi bayanin falalar wanda ya fi kyautata wa iyalinsa, kuma wannan ya kamata ya zama wani muhimmin ginshiƙi a yadda muke koya wa samari ma’anar zama miji.

Idan kuma mace ta zo wajen iyayenta tana kuka, bai kamata a fara tunanin abin da mutane za su ce ba. Ya kamata a fara da sauraron ta. Me ya faru? Shin abin ya faru sau ɗaya ne ko ya zama al’ada? Shin akwai damar gyara? Shin mijin yana shirye ya gyara? Shin akwai wani haɗari da ke buƙatar a kare ta daga gare shi? Shin yara suna cikin matsalar? Shin akwai dattawa ko mutanen kirki daga ɓangarorin biyu da za su iya shiga cikin hikima?

Za mu ci gaba.

By ukarofi

Leave a Reply