Yadda ’yan haɗaka a Nijeriya suka kafa sabuwar jam’iyya mai neman rijista a INEC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Kungiyar gamayyar jam’iyyun adawa ta Nijeriya (NNCG), a ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya nemi hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa da ta yi wa musu rajistar sabuwar jam’iyyar siyasa.

ƙungiyar ta nemi INEC ta yi wa jam’iyyar da ta kira da All Democratic Alliance (ADA) rajista kuma hukuumar ta sanar a ranar Juma’a cewa ta karɓi takardar neman izinin rajistar sabuwar jam’iyya mai ɗauke da kwanan watan 19 ga watan Yuni wadda kuma shugaban jam’iyyar ADA, Akin Ricketts da sakatarenta na ƙasa Abdullahi Elayo, suka sa wa hannu.

“Mun rubutu wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) cikin mutuntawa wannan takarda ce domin neman a yi mana rajistar All Democratic Alliance a matsayin jam’iyyar siyasa.

“Wannan ya biyo matakin da ƙungiyar gamayyar jam’iyyun adawa suka ɗauka na ɗaukar nauyin rajistar jam’iyyar.

“Sunan jam’iyyar zai zama All Democratic Alliance da za a riƙa kira da ADA kuma takenta shi ne adalci ga kowa.

“Babban ofishin jam’iyyar yana rubuce a ƙasar wannan wasiƙa.

“Kuma mun sanya tambarin jam’iyyar da kuma yin bayani game da ma’anar ma’anonin alamomin da kuma na launukan da ke ɗauke da shi da na masarar da ke jikin jam’iyyar.

“Mun kuma sanya ƙarin bayani game da manufofin jam’iyyarmu da kundin tsarin mulkinmu wanda ya samar mata da tsarin doka da maishe ta ƙungiya da zai riƙa yi wa ayyukanmu jagoranci kamar yadda yake ƙunshe a sashe na 40 da 222 na kundin tsarin mulkin Nijeriya da sashe na 75 na kundin dokokin zaɓe na (2022) da tsarin dimokradiyya ta duniya.

“A tare da wannan wasiƙa za ka samu tsarin tutar jam’iyyarmu wanda ke nuna suna da takaitawa da take da manufofi da kundin tsarin mulki da zaman da muka yi a matsayin ƙungiya.

“A yayin da muke jiran ji daga gare ku wajen cikar burinmu, muna jaddada girmamawarmu a gare ku.

“Mun gode,” duk a cikin takardar.

Baya ga Atiku akwai sauran ‘yan siyasa da ke cikin wannan tafiya da ta haɗa da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da takwaransa na jihar Ribas, Rotimi Amaechi da Umar Ardo, tsohon mataimaki ga tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, kuma wanda ya shirya taron ƙungiyar masu fafutukar dimokraɗiyya.

Atiku wanda mamba ne na jam’iyyar PDP wanda ya yi mata takarar shugaban ƙasa a shekarar 2019 da 2023 da yayin da El-Rufai yake a jam’iyyar SDP da Amaechi wanda yake a jam’iyyar APC.

Wannan takardar neman rajista ta sabuwar jam’iyyar ya kawo ƙarshen ce-ce-ku-cen da ake yi na cewa gamayyar jam’iyyun adawar za su yi takara ne a ƙarƙashin jam’iyyar ADC ko SDP.

A yanzu dai Nijeriya na da jam’iyyu kusan 18. Idan aka yi wa sabuwar jam’iyyar ADA rajista, adadin zai dawo zuwa 19.

Gamayyar jam’iyyun adawa sun yi zaman su na farko ne wanda wasu shugabannin jam’iyyun adawa suka halarta a ranar 20 ga watan Maris a Abuja, inda suka bayyana shirinsu na ƙalubalantar shugaban ƙasa Bola Tinubu a 2027.

Taron ya samu halartar Babachir Lawal, tsohon sakataren gwamnatin Kano (SGF) da Segun Sowunmi, tsohon mai magana da yawun ƙungiyar yaƙin neman zaɓe na Atiku Abubakar Campaign Organisation da Salihu Lukman, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na yankin Arewa maso yamma da Adamu Waziri da Peter Ameh da Soni Monifade da El-Rufai da Yunusa Tanko wanda ya wakilci Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023.

A yayin da yake magana ga ‘yan jarida bayan kammala taron, Atiku, wanda ya sha kaye a hannun Tinubu a shekarar 2023, ya zargi shugaba Tinubu da ƙaddamar da dokar ta-ɓaci a jihar Ribas kwanaki biyu kafin taron. Ya kuma buƙaci da ya soke wannan mataki da ya ɗauka.

“Muna yin Alla-wadai da wannan abu da kiran ‘yan Nijeriya da su nuna ƙin amincewarsu kan wannan ƙoƙari na yi wa kundin tsarin mulki karen tsaye da dimokraɗiyya.”

Da aka yi masa tambaya kan ko gamayyar jam’iyyun adawar za su ƙalubalanci APC a 2027, sai Atiku ya ce; “E, wannan shi ne matakin da ƙungiyar adawa ke ɗauka domin ƙalubalantar APC a 2027.”

By ukarofi