Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamiɗo, ya bayyana cewa a shirye yake ya shiga kowace haɗaka da nufin kawar da Shugaba Bola Tinubu daga mulki a shekarar 2027.
Lamiɗo ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a ƙarshen mako.
Yayin da yake sukar gwamnatin Tinubu da zargin gazawa da rashin ƙwarewa, Lamiɗo ya jaddada buƙatar kawar da jam’iyyar mai mulki ta APC daga mulki.
Fitaccen jigon jam’iyyar adawa ta PDP, ya ce a shirye yake ya shiga kowace irin ƙungiya ko haɗaka, “komai sunanta”, matuƙar za a kawar da gwamnatin yanzu daga mulki.
Ya ce: “Ni ɓangare ne na kowace haɗaka, komai sunanta, da nufin kawar da wannan gwamnati marar ƙwarewa, mai kawo rashin tsaro, da ke raba Nijeriya tsakanin Arewa da Kudu. Zan shiga kowace haɗin gwiwa domin wannan manufa.”
