Yadda za a gyara wasu kura-kurai a cikin kwalliya

Daga GIMBIYA RAHMA

A wasu lokuta mutane kan aikata kura-kurai da dama wajen tsarin kwalliyar fuskarsu. Yayin da waɗansu kan yi haka saboda sauri, waɗansu kuma rashin sanin yadda ya kamata su yi kwalliyar ce ke jawo musu haka.

Koma wanne dalili ke jawo haka, ya kamata mace ta riƙa tanadar wa kanta isasshen lokaci don yin kwalliya, hakan ba zai yiwu ba sai kin zama mai tsara lokacinki a kullum. Kuma dole ki nemi madubi mai kyau. Abu na ƙarshe kullum ki riƙa neman shawarar ƙwararru. Kula da yadda za a tsara kwalliya abu ne da ya zama dole, musamman a wannan zamani da kowacce mace ke ƙoƙarin a gan ta kamar budurwa.

Ga kaɗan daga cikin kura-kuran da yadda za a gyara su:
Mata da yawa kan shafa hoda ba tare da la’akari da zavar wacce za ta dace da fatarsu ba. Yawanci jar hoda takan yi wa fata mai duhu kyau, amma ita ɗin ma dole sai mace ta nemi lambar da za ta yi daidai da fatarta. Idan za ki shafa hodar ki shafa ta wajen kasan idonki da wuraren hancinki zuwa kumatunki, sannan sai ki ɗan goga a saman goshinki. Amma idan kina shafawa a ƙasan idonki ki kula da kyau don kada hodar ta tava miki gashin ido. Akwai buƙatar ki tabbatar kin dirje ta yadda za ta bi fatar fuskarki sosai. Kada ki bari ta yi miki dabbare-dabbare.

Mata da yawa ba su fara la’akari da yanayin gashin girarsu mai yawa ne ko kadan kafin su kai ga zizara jagira. Za ki fara da zaɓar jagirar da za ta dace da gashin girarki. Idan har gashin girarki mai yawa ne, kamata ya yi ki gyara shi ta hanyar taje shi ya kwanta tare da zizara ’yar jagira kaɗan a kai. Haka waɗansu sukan yi kuskure wajen rage yawan gashin girarsu, inda suke aske fiye da yadda ya kamata. Idan har za ki gyara gashin girarki ki yi shi da natsuwa ko ki nemi wanda kika san ya ƙware ya yi miki.

Mata da yawa kan yi kuskuren zaɓen launin da ya dace su shafa idan an zo batun kwalliyar kan ido. Kuma waɗansu ba tare da sanin abin da ya dace su yi ba sukan shafa kwalliyar har ta yi yawa a kan idon. Abin damuwar shi ne idan har kwalliyar ta yi yawa ba za a ɗauki lokaci ba za ta fara zazzagowa ta zama wani abu daban. Na san waɗansu sukan zavi launin da zai yi daidai da suturar da ke jikinsu, amma ki sani ba kowanne launin aishado ne don ya yi daidai da launin suturarki za ki sanya kai-tsaye ba. Akwai buƙatar idan har kin san launin bai fiye karɓarki ba a yi masa haɗi da wani launin yadda zai ba da wani launi na daban sannan ya fito da kwalliyarki sosai.

Shi ma shafa jambaki da layin da ake ja a ƙasan leɓe suna da nasu tsarin. Kamata ya yi bayan kin shafa jambakin da kika san ya yi daidai da launin jikinki sannan kuma kika shafa shi daga cikin leɓen yadda ba zai fito waje ba. Idan kika gama sai ki ɗauko ‘ip liner’ (sunan da ake kiran abin da ake jan layin leve da shi) wanda zai yi daidai da irin jan bakin da kika shafa sannan ki ja, amma akwai buƙatar jan layin ya zama ɗan siriri yadda ba zai fito ya yi yawa daga wajen leɓenki ba.

Kuskuren da waɗansu mata ke yi shi ne, yadda suke ɗaukar jagira su zane ƙasan leɓansu da ita a maimakon ‘lip liner.’ Mun sani a lokacin da kika shafa yakan yi kyau na awa ɗaya zuwa biyu, amma da ya wuce haka jambakin ya fara fita to kwalliyar za ta canja sunanta zuwa wani abu daban.