Ko mace na da damar sakin mijinta? (2)

Daga AISHA ASAS

Abin fahimta a nan dai shine, za ta fanshi kanta da kuɗin sadaki ko kuɗin da mijinta zai yi wani auren. Idan kuwa aka tsaya akan wannan, ta kuma kawo kuɗin, mijin ya karva, to malamai mafi rinjaye sun tabbatar ta saku ko da bai furta ba, dukiyar ta zama saki daga gareta, sai dai ana son ya furta ne don samun damar yin kome idan buƙatar hakan ta taso. Kuma idan haka ta kasance, ɗaya ta ke da wadda miji ya sake ta don karen kansa.

Sai dai idan har ba ra’ayi na karan kai ba, akwai ababe da suka rataya kan miji, idan bai sauke su ba, mace na da damar neman rabuwa idan ta kasa haƙuri, kamar ci ko biyan buƙata, idan ta kasa jure wa ta nemi rabuwa, to bata buƙatar ba shi ko ƙwandala, haƙƙin na ta da ya kasa sauke wa ne hujjar da za ta ƙwace kanta, kuma irin wannan hukuma ce za ta yi mata, wato alqali na shari’ar Musulunci. Idan har tana da gaskiya, za a warware auren ba tare da ko Nairanta ta yi ciwon kai ba.

Daga ƙarshe zan ce, haƙuri bai taɓa yawa ba, mata da mazan muna buƙatar shi, sau da yawa rashin sa ne ke kai ga sakin. Mata kuwa, ku ji tsoron Allah, sau da yawa dalilan da ke sa mu nemi sakin ba ƙwaƙwara ba ne, dalili ne na ruɗin zuciya da bauta wa sheɗan.

Wasu matan za su haɗu da wasu mazan ne a waje, sai su nuna buƙatar aurensu, don haka sai idonsu ya rufe, zuciyarsu ta ruɗu da irin kulawa da soyayyar da suka nuna masu, ba tare da dogon tunani ba sai su yanke hukuncin ya fi na su mijin.

Namiji tamakar ɗan siyasa ne a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe, alƙawaruka, daɗin baki ba irin wanda basa yi ma ku, fatansu kawai ki amince da su, don haka za su yi ƙoƙarin shimfiɗa ma ki kyakyawa, su bove munmuna, soyayya tamkar kina cikin wani fim na Indiya, ke kuwa sai ki sakakance kin samu mijin littafi. Ba za ki gane ba ki da wayo ba, sai ya kawo ki gidansa, an zama ɗaya, sannan za ki gano wasan kwaikwayon da ya shirya ma ki a lokacin da ki ke gida.

Duk da wannan masaniya da ki ke da shi, bai hana wani zuwa ya sake shirya ma ki wani fim ɗin da zai sa ki rena ƙoƙarin mijinki, wanda akwai yiwar idan kin shiga na sa gidan ko rabin abin da ki ke samu a gidan mijinki ba za ki samu ba.

Don haka na ke kira ga mata da kakkausar murya, kada ku biye wa sha’awar zuciya wurin bin hanyar rabuwa da mazajenku. Babu mijin littafi a wannan lokaci kamar yadda ba matar littafi, don haka idan kin samu mai ɗan dama-dama ki yi maleji da abin ki, kamar yadda yake maneji da ke. Ku taru ku rufa wa juna asiri, ku sa haƙuri don cin ribar zaman. Amma ki sawa rainki, idan har ki ka biye wa sha’awar zuciya da ruɗin shaiɗan na cewa za ki samu irin soyayyar da ki ke gani a finafinai, to fa akwai babban kaso na yiwar za ki yi rayuwa ba tare da miji ba, domin za ki dinga shiga da fice ne a gidajen magidanta har ki kai lokacin da ba mai ɗauka.

Idan har za ki hau wannan mataki na hulu’i, ki tabbatar dalilinki karɓaɓɓe ne ga duk wanda yake son gaskiya. Ki yi don tsoron shiga fushin Allah, ki tabbatar dalili ne da idan kin kawar da kai kansa za ki iya shiga halin da ba zai haifarmaki ɗa mai ido ba a gobenki.