Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata ƙungiya mai zaman kanta ta Rotary International, ta shirya taron horar da ’yan jarida kan dabarun faɗakar da al’umma kan yadda za a rage yawan mace-macen mata masu juna biyu da ƙananan yara.
Taron bitar ya mayar da hankali ne kan ilmantar da ’yan jarida daga kafofin yaɗa labarai na cikin gida da na waje kan hanyoyin faɗakar da al’ummar yadda za a rage wannan matsala.
A jawabinta ga mahalarta taron na kwanaki uku, jami’ar ƙungiyar Rotary, Mary Alaje, ta bayyana cewa babban burin ƙungiyar shi ne inganta lafiya da walwalar mata da ƙananan yara da matasa a Nijeriya.
Mary Alaje, ta kuma bayyana cewa taron horarwan na daga cikin kokarin da Rotary na rage mace-macen mata da ƙananan yara ta hanyar ilmantar da ma’aikatan yada labarai yadda za su isar da sako ga jama’a yadda ya dace.
Don haka ta jaddada muhimmancin bitar wajen ganin an rage matsalar.
