Yajin aikin ASUU: Gwamnatin Nijeriya za ta fara aiwatar da tsarin ‘ba aiki, ba albashi’

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Alamu na nuni da cewa watakila Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da manufar ‘ba aiki, ba albashi’ domin daƙile yajin aikin da Ƙungiyar Malaman jami’o’i (ASUU) ta dade tana yi.

Matakin da gwamnati ta ɗauka ya biyo bayan sanarwa da wasu wasiƙu da hukumar da ke yajin aikin ta aike wa da wasu ƙungiyoyin jami’o’in da suka haɗa da kwamitin haɗin gwiwa na JAC wanda ya ƙunshi NASU da SSANU.

Majiyoyin da suka yi magana kan lamarin sun ce gwamnatin Nijeriya ta yi amfani da manufar tsayar da albashin ne a watan Maris ɗin 2022.

Shugaban NAAT, Ibeji Nwokoma wanda ya tabbatar da lamarin ya ce ba a biya mambobin ƙungiyarsa cikakken albashin su na watan Maris ba.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Nwokoma ya kuma zargi FG da yin watsi da duk wasu takardu da wasiƙu da aka aika na neman magance matsalolin da ƙungiyar ta bijiro da su.

A cewar Nwokoma, maimakon gwamnatin Nijeriya ta gayyaci ma’aikatan da ke yajin aikin domin tattaunawa a kan lamarin, sai kawai ta aiwatar da manufofinta na ‘ba aiki, ba albashi’.

Ya kuma ƙara da cewa mambobin ƙungiyar ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen neman ingantaccen yanayin aiki ga ma’aikata da ɗalibai ba.

“Yau, mun shiga mako na biyar na yajin aikin gargaɗi, makwanni biyu na farko, sannan muka kwashe makwanni huɗu.

“Abin takaici, kamar yadda muke magana, gwamnati ba ta kula da duk sanarwar yajin aikin ba da duk wasiƙun da muka rubuta musu har yau.

“Har ila yau, gwamnati ba ta gayyace mu ba, ko kuma ta ga ya dace ta gayyace mu wajen tattaunawa a kan teburi, domin a samo mafita ba.

“Kuma abin takaici, sai kawai gwamnati ta yanke shawarar dakatar da albashin mu, ta hanyar amfani da tsarin ba aiki, ba albashi.”