‘
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Yan Kwada da ke cikin ƙauyen Faruruwa a ƙaramar hukumar Shanono ta Jihar Kano, da yammacin jiya Lahadi, inda su ka sace mata biyar, ciki har da masu shayarwa.
Mazaunin yankin ya shaida wa daily trust cewa maharan sun iso da yawa ɗauke da muggan makamai, inda suka yi wa gidaje da dama dirar mikiya kafin su tafi da waɗanda su ka sace din.
“Sun zo kamar yadda suka saba, suna harbi a iska sannan suna ɓalle ƙofofi suna shiga gidaje. Sun sace mata biyar, ciki har da masu shayarwa” in ji majiyar.
Sai dai, majiyar ta ƙara da cewa mata biyu daga cikin waɗanda aka sace sun dawo, yayin da sauran uku ke hannun masu garkuwa da su har yanzu.
Rahotanni sun nuna cewa wannan harin na zuwa ne makonni ƙasa da guda bayan da sojoji suka yi musayar wuta da ‘yan bindiga a yankin, inda aka kashe 19 daga cikinsu.
Rahoton ya ƙara da cewa mazauna yankin Faruruwa da sauran kauyukan kan iyaka tsakanin Kano da Katsina na ci gaba da rayuwa cikin tsoro da fargaba saboda hare-haren ‘yan bindiga da ke maimaituwa a yankin.
Bincike ya nuna cewa Wasu ƙauyuka da dama an bar su babu kowa, yayin da mazaunansu suka tsere zuwa garin Faruruwa ko kuma birane domin neman tsira da kariya.
