
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya taya tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau murnar cikarsa shekaru 70 a duniya.
Tinubu, a wata takarda daga Kakakinsa Bayo Onanuga, ya jinjina wa Shekarau bisa gudumawarsa acikin al’umma musamman a fage siyasa, wanda ya faro tun daga malamin makaranta har zuwa babban sakatare a ma’aikatar ma’aikata ta jiharsa, gabanin shiga harkokin siyasa a shekarun farko na 2000s.
Shugaban ƙasar ya tuno lokacin da Shekarau ya lashe zaɓen gwamna a shekarar 2003, inda ya doke gwamna mai ci na a wancan lokaci, lamarin da ya taimaka masa riƙe muƙamin har na tsawon wa’adi biyu.
Daga bisani a 2014 Shekarau ya zama Ministan Ilimi na tsawon shekara ɗaya, sannan ya kuma yi riƙe muƙamin Sanata na Kano ta Tsakiya daga 2019 zuwa 2023.
Kazalika, Tinubu ya yi godiya ga Sanata Shekarau bisa hidimarsa ga ƙasa a matsayinsa na masani kuma ɗan siyasa, yana mai masa fatan Allah Ya ƙara masa lafiya ta yadda zai cigaba da hidimta wa al’umma.
