Gwamnatin Tarayya ta rage kuɗin hajjin 2026 zuwa miliyan N7.6

Spread the love

Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta sanar da rage kuɗin aikin Hajji na shekarar 2026 ga maniyyata daga sassa daban-daban na ƙasar, inda aka samu sauƙin kuɗi idan aka kwatanta da na bara.

A sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce maniyyata daga yankin Borno da Adamawa za su biya N7,579,020.96, maimakon N8,327,125.59 da suka biya a 2025, wanda hakan ke nuna an samu ragin kusan N748,104.63.

Haka kuma, masu niyyar tafiya daga yankin Arewa za su biya N7,696,769.76, wanda ke nuna ragin N760,915.83 daga kuɗin bara da ya kai N8,457,685.59.

A ɓangaren masu tafiya daga Kudancin ƙasar kuwa, farashin da aka sabunta na 2026 shi ne N7,991,141.76, raguwar N792,943.83 daga kuɗin 2025 da ya kai N8,784,085.59.

Hukumar ta ce wannan ragin kuɗi na zuwa ne sakamakon ƙoƙarin da gwamnati da hukumomin da abin ya shafa suke yi domin sauƙaƙa wa alhazai, tare da tabbatar da cewa farashin bai zama matsi ga masu niyyar gudanar da ibadar ba.

NAHCON ta kuma tabbatar da cewa za ta cigaba da aiki tare da hukumomin Saudiyya da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da shirin hajji 2026 ya gudana bisa nasara da tsari.

By Babaji