
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Umar Raɗɗa na Jihar Katsina, ya bayyana nasarar da Farfesa Chukwuma Soludo ya samu a matsayin wata gagarumar nasara da ta samo asali daga jajircewa, hangen nesa a jagoranci, da kuma amincewar da ƴan Jihar Anambra suka gina a gare shi tsawon shekaru.
A sanarwar da Babban Sakataren yaɗa labaran gwamnan, Muhammad Kaula ya fitar, gwamnan ya ce sakamakon zaɓen, wanda aka kammala da tazara mai yawa, ya nuna irin gamsuwa da goyon bayan da jama’a ke da shi ga irin salon jagoranci na Gwamna Soludo da tsarin gwamnatin sa mai cike da sauye-sauye, da kuma jajircewarsa wajen kyautata shugabanci.
Gwamna Raɗɗa ya lura cewa gagarumar nasarar da Farfesa Soludo ya samu a zaben ranar Asabar ta sanya shi zama gwamna na uku a tarihin siyasar Jihar Anambra da ya sake lashe wa’adin mulki karo na biyu — abin da ke nuna ingancin aikinsa da amincewar jama’a da jagorancinsa.
“Nasaran da Gwamna Soludo ya samu ba kawai nasarar siyasa bace, illa tamkar tabbaci ne na ingancin aiki, hali nagari, da kuma sadaukarwa wajen yi wa jama’a hidima. Kwarewarsa wajen fassara ra’ayoyi zuwa sakamakon da ake iya gani ya bambanta shi da yawancin shugabanni a Najeriya”, inji Raɗɗa.
Gwamnan Jihar Katsina ya kuma yaba wa kokarin Soludo wajen dawo da martabar Jihar Anambra a matsayin cibiyar kirkire-kirkire, ci gaban ababen more rayuwa, da bunkasar tattalin arziki. Ya bayyana shi a matsayin gwarzon shugabanci mai ilimi wanda ya tabbatar da cewa ilimi idan aka hada shi da tausayi da ladabi, yana iya sauya al’umma.
Raɗɗa ya kuma jinjinawa jama’ar Jihar Anambra saboda yadda suka gudanar da kansu cikin lumana a lokacin zaben, da hukumar INEC da jami’an tsaro saboda tabbatar da sahihin da gaskataccen tsari. Ya ce wannan ya nuna irin cigaban da ake samu a siyasa da dimokuraɗiyyar Najeriya.
A cewar Raɗɗa, sake zaben Farfesa Soludo ya bashi damar ci gaba da aiwatar da shirye-shiryensa da manufofinsa na inganta rayuwar jama’a. Ya bukace shi da ya ci gaba da aiwatar da sauye-sauye cikin tawali’u, hikima, da hadin kai.
“A matsayinsa na na aboki kuma dan uwana a Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Farfesa Soludo ya nuna jajircewa wajen tabbatar da hadin kan kasa da cigaba. Salon mulkinsa wanda ya ta’allaka kan ingantaccen tattalin arziki, gaskiya da amana, na ci gaba da zama abin koyi ga sauran shugabanni a fadin kasar nan,” in ji Radda.
Gwamna Radda ya kuma bukaci jama’ar Jihar Anambra da su ci gaba da mara wa gwamnan su baya, yana tabbatar musu cewa wannan sabuwar damarka za ta haifar da karin ci gaba da yalwar arziki a jihar. Ya bayyana kyakkyawan fata cewa Gwamna Soludo zai ci gaba da gina gada ta hadin kai, ba kawai a Anambra ba, har ma tsakanin jihohi a fadin Najeriya.
Ya kuma bayyana shirinsa na ci gaba da hada kai da gwamnatin Jihar Anambra musamman a fannoni kamar ci gaban noma, karfafa sana’o’in dogaro da kai, ilimi, da gina cibiyoyin gwamnati — fannonin da duka gwamnonin ke da sha’awa a cikinsu.
“A madadin gwamnatin da jama’ar Jihar Katsina, ina taya dan uwana kuma abokina, Farfesa Chukwuma Charles Soludo, murnar wannan tarihi da nasara mai daraja. Allah Ya ba shi ƙarfi, hikima, da jagorancin nagari yayin da yake ci gaba da yi wa jama’arsa hidima da hangen nesa da jarumtaka”, inji Raɗɗa.
