Sulhu: ‘Yan bindiga sun sako mutane biyar a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Sakamakon sasanci da wasu ƙananan hukumomi na Kudancin jihar, ƴan bindiga a Ƙaramar Hukumar Sabuwa sun saki mutane biyar waɗanda dukkan su ƴan asalin yankin garin Maska ne.

‘Yan bindigan sun miƙa mutanen ne a garin Sabuwar da ke karamar hukumar Sabuwa inda suka miƙa su ga Magajin Garin Maska Alhaji Abdullahi Umar.

Shugaban karamar hukumar Funtua Hon Abdulmutallaf Suleiman Goya wanda shine yayi ta kaiwa da komowa wajan ganin an sako mutanen ya ce mutanen da aka sako Yan asalin garin Maska a karamar hukumar Funtua.

Ya bayyana cewa, duk da suna cikin koshin lafiya amma duk da haka aika da su zuwa babban asibitin Sabuwa domin ƙara duba lafiyar su.

Shugaban karamar hukumar ya ce zai cigaba da bin hanyoyin da ta dace wajan sako sauran mutanen yankin.

Hon. Suleiman Goya ya kara da cewa mutanen da suka ɗauki tsawon watanni ukku a hannun Yan bindigan,an sako su ba tare da biyan ko kobo ba a matsayin kudin fansa.

Ya nuna gamsuwa ga yadda ƴan bindigan suka mutunta yarjejeniyar wajan sako mutanen da sukai garkuwa da su bata da gindaya wasu sharuɗɗa ba ko bayin kuɗin fansa ba.

Shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa yana sane da akwai wasu wurare ɗai ɗai ku da ake samu hare haren yan bindiga musamman a yankin Maska inda ya ce “zan cigaba da tuntuɓar ƴan bindiga domin ganin an sami dawamammen zama lafiya a karamar hukumar Funtua.”

Ya kuma jaddada ƙudirin sa na tabbatar da zaman lafiya da kawo cigaba a karamar hukumar,sai yayi kira ga masu ruwa da tsaki na yakin da su bada tasu gudunmawa wajen kawo zaman lafiya da cigaban al’umma.

Suleiman Goya ya yi godiya ga Gwamna Dikko Raɗɗa, sarakunan gargajiya, Malaman Addini da sauran masu ruwa da tsaki a yankin bisa irin gudunmawar da suka bada wajan cigaban karamar hukumar.

A jawabinsa Magajin Garin Maska Alhaji Abdullahi Umar ya jinjina wa shugaban karamar hukumar Funtua bisa ƙoƙarin da yayi wajan tabbatar da sako waɗannan mutane da kula da lafiyarsu.

By Babaji