’Yan bindiga na ci gaba da kashe kansu a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wani ƙazamin rikici ya ɓarke tsakanin dabar ‘yan bindiga a Jihar Katsina, rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan bindinga 20 da ba sa jituwa a tsakaninsu.

Daga cikin mutanen da suka rasa rayukansu akwai fitattun shugabannin ‘yan bindigar da mabiyansu.

Rikicin ya afku da sanyin safiyar Alhamis ɗin nan, rahotanni sun bayyana cewa ɓarayin dajin sun gwabza faɗan ne a yankin ɗan Ali da ke ƙaramar hukumar ɗan Musa ta jihar Katsina.

Wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya bayyana cikakken bayani kan yadda rikicin ya ɓarke ta hanyar wani saƙo da ya wallafa a shafin ɗ (Twitter) inda ya bayyana cewa rikicin ya faru ne tsakanin dabar Mai Nore da dabar ‘yan ta’adda ta Buzaro. 

“Da safiyar yau ne aka gwabza ƙazamin faɗa tsakanin ‘yan dabar Mai Nore da dabar Buzaro a yankin ɗan Ali,” inji Makama.

Ya ci gaba da cewa “A cewar majiyoyin leƙen asiri, rikicin ya yi sanadin salwantar rayuka, inda aka gano gawarwaki sama da 20 a wurin.” 

Shaidun gani da ido sun bayyana rikicin ‘yan ta’addar a matsayin mafi muni, inda aka ɗauki tsawon lokaci ana jin rugugin ƙarar bindigogi tare da harbe-harbe a tsakaninsu.

Wasu rahotannin sun bayyana cewa ‘yan bindiga da dama sun samu raunuka a yayin arangamar. 

Masana harkokin aikace-aikacen ‘yan bindinga sun bayyana cewa rikicin ɓarayin dajin, bai rasa nasaba a kan ƙoƙarin da kowace daba ko ƙungiya ke yi na ganin ta kama iko da yankin, don samun damar mallakar albarkatun ƙasa da na jama’a a yankin.

By ukarofi