Yadda rikici zai kicime bayan Iran ta kai wa Isra’ila hari

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ricikin da ya ɓarke tsakanin ƙasar Isra’ila da Iran na cigaba da jan hankulan al’ummar duniya.

Rikicin ya sa mutane da dama, ciki har da shugabannin duniya suke hasashen cewa idan yaƙin ya ɓarke tsakanin ƙasashen biyu zai iya kawo babban tashin hankali da koma-baya a Gabas ta Tsakiya.

Wasu masu sharhi suna ganin illar rikicin ba za ta tsaya a Gabas ta Tsakiya kaɗai ba, za ta iya mamaye duniya baki ɗaya.

A shekarun baya, ƙasashen biyu sun kasance ƙawayen juna har zuwa juyin juya halin addinin Musulunci da ya faru a Iran a shekarar 1979, wanda ya kawo sabon tsarin mulkin da ya ɗauki adawa da Isra’ila a matsayin wani muhimmin al’amari.

Tun da aka fara zaman doya da manja tsakanin ƙasashen biyu, sun kasance suna nuna wa juna yatsa da cacar baki.

Amma duk da zaman ‘ba a ga maciji’ tsakanin su, ba a samu kai mummunan hari ba sai wannan karon, inda Iran ta harba sama da rokoki masu linzami sama da 200 a yankin Isra’ila.

Ana cigaba da mayar da martani game da hare-haren rokokin da Iran ta ƙaddamar kan Isra’ila, inda manyan ƙasashe ke jaddada matsayinsu na cewa Isra’ila na da damar kare kanta, duk da kuwa ita ta fara tsokana a lokacin da kashe shugaban HAMAS, Ismail Haniye.

Tuni manyan ƙasashen kamar Birtaniya, firaministan ƙasar Keir Starmer ya tabbatar wa takwaransa na Isra’ila Benjamin Netanyahu cikakken goyon bayansa, tare da yin tir da matakin Iran na ƙaddamar da hare-haren rokokin. 

Firaminista Starmer ya ce babu wanda zai amince da matakin Iran na harba makamai masu linzami kusan 200, kuma abin da mahukuntan Iran suke buƙatar gani shi ne kassara ƙarfin yaƙin Isra’ila. Shi ma Firaminista Anthony Albanese na ƙasar Australiya, na cikin shugabannin ƙasashen duniya da suka yi tir da matakin na Iran.

A cikin sanarwar da ministan harkokin wajen Isra’ilan Israel Katz ya fitar, Isra’ila ta nuna mamakin yadda Sakatare Janar na Majalisar ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya gaza yin tir da wannan hare-hare na Iran tare da haramta masa sake shiga ƙasar.

Gwamnatin Isra’ila ta yi barazanar cewa za ta ɗauki fansa game da makaman roƙa da Iran ta harba zuwa ƙasar.

A hannu guda kuma Iran ɗin ta ce muddun Isra’ila ta yi yunƙurin kai mata hari, za ta lalata kayayyakin more rayuwan a babban birnin ƙasar na Tel Aɓiɓi ɗin.

Haka zalika, Iran ta ce za ta kai hare-hare a kan “muhimman kadarorin” Isra’ila idan har ta mayar mata da martani.

Babban Hafsan Tsaron Iran, Manjo Janar Mohammad Bagheri ne ya yi wannan gargaɗin, inda ya yi barazanar ƙaddamar da hare-haren da zarar Isra’ila ta ce musu kule.

“Idan Isra’ila ta cigaba da hare-haren da take yi, ko kuma ta nemi ta taɓa mutuncinmu da ‘yancin ƙasarmu, lallai za mu maimaita irin waɗannan hare-haren da muka yi, ko kuma ma waɗanda suka fi zafi domin za mu kai hare-haren ne a kan dukkan kadarorinta,” inji Bagheri.

Ya ce dakarun Iran ‘Reɓolutionary Guard Corps’ a shirye suke domin kare ƙasar, da kuma maimaita irin hare-haren da suka kai a daren Talata.

Yadda ricikin ya samu asali:

Juyin juya halin musulunci Iran a shekarar 1979 ya nuna wani sauyi a dangantakar Iran da Isra’ila. Hamɓarar da ɗaular Pahlawi tare da kafa jamhuriyar Musulunci a ƙarƙashin Ayatullah Khumaini ya haifar da koma baya ga manufofin ƙetare da kuma mahangar Iran gabaɗaya. Duk da haka, a cikin shekarun farko, Iran da Isra’ila sun ci gaba da dangantaka.

Isra’ila da Iran dai na ganin ya dace su tunkari gwamnatin Iraƙi ta Saddam Hussein. Iraki na daga cikin ƙasashe uku na Larabawa da ke fama da rikici a lokacin.

A lokacin yaƙin Iran da Iraki tsakanin 1980-88, an bayar da rahoton cewa Isra’ila ta riƙa bi ta bayan fage tana sayen makamai na dala miliyan 500 a duk shekara, kamar yadda jaridar The Obserɓer ta Birtaniya ta bayyana.

Mujallar Time ta bayyana cewa, Isra’ila har ma ta kafa asusun ajiyar banki na Switzerland. Dakarun Isra’ila a birnin Kudus sun yi fatan samar da makaman da za ƙarfafa sojojin Iraƙi wajen yaƙar Iran domib kawar da sabuwar gwamnatin Ayatullah.

Dangantaka na ɓoye ya ci gaba har zuwa wani lokaci bayan yaƙin Iran da Iraki ya ƙare, amma alaƙar ta yanke bayan nan.

Iran, wacce a yanzu ƙasa ce mai tsarin mulki irin na musulunci, ta ɗauki Isra’ila a matsayin mai mamaye ƙasar Falasɗinu. Har ila yau Iran tana yiwa Isra’ila laƙabi da ‘ƙaramar Shaiɗaniya, wanda a Turance suke ce mata “Little Shaidan”, yayin da ake kiran Amurka da “Babbar Shaiɗaniya”.

ƙasar Shia ta Iran ta so ta zama cibiyar wutar lantarki ta Gabas ta Tsakiya, kuma ta fara ƙalubalantar Saudiyya, Makkah na Sunni. Haka kuma tana ganin Isra’ila da Amurka suna tsoma baki cikin harkokin yankin.

Sabuwar gwamnatin Iran ta yanke duk wata alaƙa ta diflomasiyya da Isra’ila, kuma ƙasar ta fara goyon bayan Falasɗinawa da sauran ƙungiyoyi masu adawa da Isra’ila. Wannan al’amari ya zama gagarumin koma baya ga Isra’ila, inda faɗace-faɗace tsakanin wasashe biyu ya haure.

A cikin wannan lokaci ne Iran ta fara tallafa wa ‘yan Shi’a na Lebanon, wanda daga baya suka ɗauki siffar Hizbullah, kamar yadda wani rahoton BBC ya bayyana.

Harin makami mai linzami da Iran ta kai ranar Talata a kan Isra’ila, a matsayin martani ne ga hare-haren da Isra’ila ta kai kan wasu manyan jami’an dakarun Hizbullah, ciki har da shugaban ta, Sayyid Hassan Nasrallah, da kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Abbas Nilforoushan da shugaban Hamas Ismail Haniyeh, wanda ta kashe a Hotal ɗin sa a birnin Tehran.

Shin rikicin zai kai ga yaƙin duniya?

Wannan rikici na yankin Gabas ta Tsakiya da tsoron yiwuwar ɓarkewar yaƙi a yankin, ya janyo tashin farashin ɗanyen man fetur a kasuwannin duniya.

Muddun wannan rikici na yankin Gabas ta Tsakiya da ake fargabar yiwuwar rincaɓewarsa ya gawurta farashin ɗanyen man fetur zai ci gaba da tashin gwauron zabi, saboda tasirin ƙasashen wajen fitar da man fetur zuwa ƙasashen duniya.

Ministan harkokin waje na ƙasar Iran, Esmail Baghaei ya zargin ƙungiyar ƙasashe bakwai masu ƙarfin tattalin arziƙi da “son zuciya da rashin dattako” dangane da sukar harin da ƙasarsa ta kai Isra’ila.

Esmaeil Baghaei ya ce “ƙasashe bakwai masu ƙarfin tattalin arziƙi musamman Amurka na ƙara ta’azzara rashin tsaro da rashin zaman lafiya a yammacin Asia” saboda yadda suke bai wa Isra’ila makamai.

A ranar Laraba ne dai ƙasashen bakwai masu ƙarfin tattalin arziƙi da suka haɗa da Canada da Faransa da Jamus da Iyaliya da Japan da Birtaniya da Amurka, a wata sanarwar haɗin gwiwa sun yi kakkausan suka dangane da harin da Iran ɗin ta kai wa Isra’ila.

Ita ma ƙasar Iran ta kira jakadun Jamus da Austria da ke ƙasar a ranar Alhamis domin su bayar da bahasi kan sukar da ƙasashensu suka yi wa Iran ɗin.

Jaridar Economic Times ta ba da rahoton fitacciyar mai hasashe, Baba ɓanga, wacce ta yi gargaɗi mai tsanani game da yiwuwar ɓarkewar yaƙin duniya na III biyo bayan ƙaruwar tashe-tashen hankula a yankin gabas ta tsakiya.

Haka shi ma shugaban Colombia, Gustaɓo Petro, kamar yadda jaridar Times of India ta ruwaito, ya yi gargaɗin yiwuwar fara yakin duniya na III daga wannan rikicin.

Ya kuma soki goyon bayan wasu ayyukan kisan ƙare dangi da manyan ƙasashen duniya ke yi.

Shugaban ya ƙara jaddada buƙatar ɗaukar matakan samar da zaman lafiya cikin gaggawa daga Majalisar ɗinkin Duniya domin kaucewa ɓarkewar yaƙiin duniya na III.

Sakataren tsaron Birtaniya Grant Shapps ya bayyana damuwarsa yana mai cewa duniya na iya shiga babban yaki da zai kai ga yaƙin duniya.

Wanda ya ke cewa matuƙar ba a dakatar da rikicin ba, akwai yiwuwar ɓarkewar rikice-rikice da za su shafi manyan ƙasashen duniya kamar China, Rasha, Koriya ta Arewa, da Iran cikin shekaru biyar masu zuwa. Wanda a cewarsa hakan ba makawa zai kai ga yaƙin duniya.

Hugh Loɓatt, wani babban jami’in siyasa a Majalisar Turai kan Harkokin Waje, ya bayyana wani ra’ayi mai sanyaya zuciya, yana mai cewa abinda ya ke zahiri shine ba za a yi yaƙin duniya na III ba.

Ya lura da cewa duk da akwai manyan rikice-rikice da tashin hankali a yankuna kamar Ukraine, Gabas ta Tsakiya, da Asiya-Pacific, amma babu alamar cewa za a yi yakin duniya saboda rikice-rikicen a wurare mabanbanta suke faruwa, cewar Times of India.

Yanzu idon duniya ya karkata ga ƙasashen biyu, inda wasu ke tambayar cewa idan Isra’ila ta mayar da martani, me Iran za ta yi a gaba?

Shin idan Iran ta mayar da gagarumin martani hakan zai kai ga yaƙin duniya na III? Lokaci alƙali!

Yayin da tashe-tashen hankula ke ci gaba da ta’azzara, wani abu ɗaya tabbatacce shi ne, ba za a taɓa warware rikicin da ke tsakanin Iran da Isra’ila ba, musamman ganin yadda aka jima da shata layi, tun bayan juyin juya halin Musulunci, wanda Ayatullahi Khomaini ya jagoranta.

Meye matsayin Nijeriya a rikicin gabas ta tsakiya?

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yi kira ga ƙasashen Iran da Isra’ila da su sanya wa zukatansu ruwan sanyi biyo bayan harin da aka kai a ranar Talata da tsakar dare.

By ukarofi