Akwai rufa-rufa da siyasa a sake fasalin Naira na Emefiele – Shonubi

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Tsohon Muƙaddashin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, CBN, Folashodun Shonubi, a ranar Laraba ya shaida wa mai shari’a Maryann Anenih na babbar kotun birnin tarayya da ke Maitama Abuja cewa akwai siyasa a sake fasalin naira da aka yi a shekarar 2022.

Shonubi wanda ya kasance mataimakin gwamnan ayyuka kafin a naɗa shi muaaddashin gwamnan CBN, amma yanzu ya yi ritaya, a martanin da ya mayar kan lauyan masu kare Olalekan Ojo (SAN) a ci gaba da sauraron shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya shaida wa kotun cewa tsohon shugaban babban bankin ya shaida masa da wasu cewa akwai rufa-rufa da siyasa a sake fasalin naira.

Emefiele, a gaban kotun mai shari’a Anenih, yana fuskantar tuhume-tuhume guda huɗu da suka haɗa da rashin biyayya ga doka da kuma aikata aikin ba bisa ƙa’ida ba wanda ya jawo raunata jama’a game da sake fasalin naira da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon ƙasa ta yi masa.

Shonubi, wanda lauya mai shigar da kara, Rotimi Oyedepo (SAN) ya jagoranta a gaban shaida, ya ce, “Sake fasalin kuɗin na shekarar 2022 shi kaɗai na ke ciki. Lokacin da muka gana da wanda ake kara (Emefiele), ya ce akwai siyasa da ruɗani a duk wannan tsarin.”

Amsar Shonubi ita ce tambayar da Ojo ya yi masa ko, a matsayinsa na ƙwararren ma’aikacin banki na CBN, yana sane da makirci da siyasa a sake fasalin naira.

By ukarofi