Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi
Sanata Shehu Buba Umar ya lura da cewar, tirka-tirkar halayen rayuwa da ‘yan Nijeriya suka tsinci kansu a ciki ya biyo bayan tsiwurwurori da kasassaɓoɓin jama’a ne da a kulli-yaumin suke kawo cikas da rashin tattibi na zamantakewa, haɗi da gurɓata lamuran rayuwa da samun kawunanmu cikin matsatsin rayuwa na rashin fasali.
Ya ce, “a matsayina na wanda ya yi yaƙina da ƙudurorin Mahalicci, zan iya yin furucin cewa, waɗannan wahalhalun rayuwa da muka samu kawunanmu a ciki, ya biyo bayan sakamakon kasassaɓoɓi da munanan halayenmu ne da suke haddasa ƙuncin rayuwa da munanan zamantakewa a tsakaninmu.
“Wannan tantibin lamari ne da ya kamata a bayyana a zahiri, maimakon a cigaba da zargin juna ko zargin a tsakanin shugabanni da mabiyansu a dukkan matakan rayuwa, maimakon yi wa lamura kallon basira domin yi masu kyakkyawar fahimtar yadda za a shawo kansu.
Sanata Umar wanda yake wakiltar mazaɓar Kudancin Jihar Bauchi a Majalisar Dattawa ta Nijeriya ya yi waɗannan tsokaci ne a saƙonsa na fatan alheri domin karrama zagayowar bikin cika shekaru 64 da samun ‘yancin Nijeriya da aka gudanar a ranar Talata da ta gabatar.
“Na shiga cikin jerin gwanon ‘yan uwa ne masu karrama wannan rana ta samun ‘yanci. A matsayina na Sanata mai wakiltar ɗaya daga cikin manyan mazuɓun zaɓe na ƙasar nan, ina da yaƙinin cewar, ɗaya daga cikin lamuran rayuwa da ya kamata a fahimtar shine na cewa, wannan ƙasa tamu tana cikin halin walagigin rayuwar yau da kullum da ba a taɓa gani ba a cikin shekaru 64 da suka shuɗe.”
Ya nanata da cewar, “Wajibi ne a durfafi sahihiyar hanya, haɗi da ɗaukar dukkan wata wacce ta dace na farfaɗo da ƙasarmu daga bacci domin amfanuwar mafi yawancin al’ummarmu bisa tunkarar ƙalubalolin da kowa zai kawo nasa gudummawar, domin tunkarar mujadalar zuwa gobe.”
Sanata Buba Umar sai ya shawarci Shugaban Bola Ahmed Tinubu da dukkan wasu shugabanni a madafun tarayya da su yi la’akarin cewa, wannan ƙunshin rayuwa da jama’a ke ciki yana buƙatar waiwaye adon tafiya, jajircewa da ƙwazo wajen kawo gudummawar sauƙaƙa rayuwar talakawan ƙasar nan.
Ya kuma lura da cewar, wasu manufofin gwamnatin tarayya sun fara kawo tagomashi, yana mai fatar hakan zai ƙara ƙarfafa ƙwiwowin shugabanni na ƙara jajircewa kan bujiro ƙarin hanyoyi da talaka zai wataya wajen samun cimma buƙatun rayuwar yau da kullum na inganta rayuwarsa.
Sanata Umar, wanda shine Shugaban Kwamitin Tsaro da Basira na Majalisar Dattawa ta ƙasa, ya kuma bayyana takaicin sa yadda fasalolin rashin tsaro dabam-dabam dake wanzuwa yau da kullum a cikin ƙasa suna yin tagomashi wa ƙalubalolin talauci ta hanyar taɓarɓarewar rayuwar talaka.
Umar, wanda ya yi wa saƙon fatan alherin nasa taken “Nijeriya A Shekaru 64, Babu Yabo Babu Fallasa”, ya ce amma bisa himmatuwar yin addu’o’i da sadaukar da ɗaukacin kawunanmu baki ɗaya, haɗi da tagomashi da dakarun mu dake bakin daga suna murƙushe matsalolin dake tasowa za mu iya tafiya kan ƙafafunmu da yardar Allah.”
Ya jinjina wa ƙoƙrin shugabannin jam’iyar siyasa ta APC a madafun ƙasa da jihohi wajen ɗinke ɓaraku dake tsakanin ‘ya’yanta, tare da gina jam’iyyar kan ta, da kuma nusar da kyawawan dabaru, shawarwari da gudanar da ayyuka tuƙuru domin tafiyar da ingantaccen jagoranci wa ƙasa.
“Idan aka juya ga mazaɓata ta Kudancin Bauchi kuwa, ina mai godiya ga Allah Subhanahu Wata’ala dangane da nasarori da muka samu damar cimmawa a cikin kyakkyawan wakilci da muke yi wa jama’a, husasan ma ta hanyoyin rarraba masu romon dimokradiyya.
“Dangane da wasu nasarori da muka cimma a halin yanzu, jagora daga cikinsu shine na ƙaddamar da ginin hanyar mota a garin Zaranda wacce aka ayyana assasa tubalin gudanar da aikinta a ranar sati mai gabatowa idan Allah ya kaimu.”
