‘
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Wasu gungun ‘yan bindiga sun kai farmaki Sabon Garin Damri da ke ƙaramar hukumar Bakura a Jihar Zamfara, inda suka yi garkuwa da mutane sama da 50.
A cewar wani mazaunin garin mai suna Malam Sani Damri ya shaidawa Blueprint Manhaja ta wayar tarho cewa ‘yan bindigar da dama sun yiwa ƙauyen ƙawanya da safiyar Lahadi ɗauke da muggan makamai suka fara bincike gida-gida.
Ya ce waɗanda aka sace galibi mata ne da ƙananan yara yayin harin.
A cewarsa, ƴan ta’addan sun yi awon gaba da ɗaruruwan dabbobi da suka haɗa da shanu, tumaki da awaki na al’ummar yankin a yayi harin.
“Kamar yadda nake magana da kai yanzu, mun gano cewa sama da mutanen mu 50 galibi mata da yara ne waɗannan ‘ƴan ta’adda suka yi garkuwa da su a lokacin da suka kai hari ƙauyen mu kuma sun yi awon gaba da ɗaruruwan dabbobin mu waɗanda suka hada da shanu, tumaki da awaki”. Ya ƙara da cewa
Ya koka da yadda aka yi watsi da yankin ba tare da tura jami’an tsaro ba, duba da irin hare-haren da ‘yan ta’addan ke kaiwa babu ƙaƙƙautawa.
“Muna cikin mawuyacin hali saboda waɗannan gungun ‘yan ta’adda suna son kashe mu ne baki ɗaya kuma har ya zuwa yanzu babu jami’an tsaro ko ɗaya da aka tura yankin namu”.
Idan dai za a iya tunawa a ‘yan makonnin da suka gabata ‘yan bindigar sun kai hari a ƙauyukan Damri, Dakko da Dambo da ke ƙaramar hukumar Bakura inda suka yi garkuwa da mutane da dama tare da kwashe ɗaruruwan dabbobi na al’ummar yankin.
Malam Sani Damri yayi kira ga gwamnatin jihar Zamfara da gwamnatin tarayya da su kawo musu ɗauki ta hanyar tura jami’an tsaro a yankin domin daƙile ‘yan ta’addan da suka addabi su domin a samu zaman lafiya.
“Muna kira ga gwamnatin Zamfara da gwamnatin tarayya da su samar da isassun jami’an tsaro a yankinmu da za su yaƙi waɗannan ‘yan ta’adda domin kare mu”. Malam Sani Damri ya bayyana.
Sai dai ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Yazid Abubakar da wakilinmu ya ci tura har zuwa lokacin haɗa rahoton.
