Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Rundunar Sojojin Nijeriya ta sanar da cewa dakarun rundunar ‘OPERATION HADARIN DAJI’ sun yi arangama da wasu ‘yan bindiga a yankin dajin Bachaka Kurya da ke ƙaramar Hukumar Gudu a Jihar Sakkwato a ranar 10 ga watan Agusta da misalin ƙarfe 11:45 na rana, inda suka rasa jami’ai huɗu.
Daraktan ayyukan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba, a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja ranar Talata, ya ce an yi wa sojojin kwanton ɓauna ne a kusa da kan iyaka da Jamhuriyar Nijar.
Ya ce, a yayin da ake gwabzawar ɓarin wuta, an kashe ’yan bindiga da dama, tare da kwato makamai da alburusai.
Sanarwar ta aara da cewa, “Gawarwakin ‘yan bindigar da aka kashe sun bayyana cewa wata ƙungiyar ta’addanci daga jamhuriyar Nijar da aka fi sani da ‘Lakurawa’ ce ke da hannu. Abin takaici, an kashe jami’ai huɗu a arangamar.
“Sauran ‘yan ta’addan sun tsere zuwa Jamhuriyar Nijar. Sai dai sojoji suna ci gaba da neman ganowa da kuma lalata duk wuraren ‘yan ta’addan.”
