CBN ya samu ƙarin Dala miliyan 553 a watan Yuli

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Babban Bankin NIjeriya (CBN) ya samu ƙaruwar kuɗaɗen da suka kai dala miliyan 553 a watan Yuli.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun babban bankin na CBN, Hakama Sidi-Ali ta fitar, yawan kuɗaɗen da aka fi samu a duk lokacin yana nuna ƙaruwar kashi 130 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar 2023.

Sidi-Ali ta ce, wannan adadi ya nuna mafi girman jimillar kuɗaɗen da ake samu a kowane wata kuma ya nuna ƙoƙarin babban bankin na ci gaba da haɓaka kuci a kasuwar canji ta Nijeriya.

A cewarta, babban ci gaban da ake samu na kuɗaɗen da ake aikawa na da nasaba ne da matakan tsare-tsare da CBN ya ɓullo da shi na bunƙasa hada-hadar kuɗi a kasuwar canji ta Nijeriya.

“Waɗannan matakan sun haɗa da ba da lasisi ga sabbin kamfanonin musayar kuɗi na ƙasa da ƙasa (IMTO), aiwatar da tsarin saye da sayarwa, da ba da damar samun kuɗi na naira a kan kari ga IMTO.

“Kuɗaɗen da ake aikawa da ƙasashen waje wata muhimmiyar hanyar samun kuɗin waje ne ga Nijeriya, wanda ke ƙara haɗa jarin ƙasashen waje kai tsaye.

Ta ƙara da cewa, ƙaruwar kuɗaɗen da aka samu na nuni ne ga nasarar ƙoaarin da CBN ke yi na kƙrfafa kwarin gwiwar jama’a kan kasuwar canji.

Daraktan ta ce, hakan wata manuniya ce ta ƙoƙarin da ake na ƙarfafa tsarin hada-hadar kuɗi na banki tare da inganta daidaiton farashi, wanda ke da matuƙar muhimmanci ga ci gaban tattalin arziki.

By ukarofi