Yadda Emefiele ya kashe biliyan N18 don buga takardun Naira biliyan ɗaya

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC) ta bayyana yadda tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) Godwin Emefiele ya kashe Naira biliyan 18 wajen buga takardar kuɗi ta Naira biliyan ɗaya kacal.

An gano hakan ne a wani sabon bincike da hukumar EFCC ta gudanar game da badaƙalar buga naira biliyan 100 da kuma acrylic blocks 5000 domin bikin cikar Nijeriya shekaru 100 a watan Oktoban 2014.

Rahoton ya bayyana cewa Emefiele ya tsallake rijiya da baya a hukumar CBN, kuma ya samu amincewa daga tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ba tare da bin ƙa’ida ba.

Kwangilar da aka baiwa wani kamfanin ƙasar Sweden Crane Currency a ranar 17 ga Satumba, 2014, an ƙara masa ƙarin farashin dalar Amurka 121,660,000.00 (N18,911,524,842.62). An fahimci cewa, kamfanin yana baiwa CBN bugu na kuɗi da sauran ayyukan da suka shafi kuɗi.

An riga an biya dala 72,996,000.00 wanda ya saɓawa kafuwar ayyuka.

Rahoton ya nuna cewa dala miliyan 39,848,991.90 ne kawai aka canjawa wuri, inda kuɗaɗen da suka kai dalar Amurka miliyan 32,716,050.00 ya canja zuwa Naira kuma aka raba tsakanin manyan jami’ai.

A cewar masu binciken, kuɗaɗen da aka ajiye na dala miliyan 32,716,050.00, an canja su zuwa Naira, aka kuma mayar da su ga reshen Nijeriya na kamfanin ƙasar Sweden, wanda ya kai Naira biliyan 5.3.

Ana kyautata zaton wannan adadin na wakiltar maƙudan kuɗaɗen da aka samu daga ƙarin kuɗin kwangilar, wanda ake zargin an yi amfani da shi wajen wadatar da manyan jami’an babban bankin Nijeriya da abokan hulɗar su.

Kamar yadda wani mai bincike ya bayyana, “An yi ƙarin farashin kwangilar ne da gangan domin amfanar wasu mutane a ciki da wajen bankin, wanda hakan ya haifar da faɗuwar Naira biliyan 5.3.”

By ukarofi