‘Yan daba sun kai hari gidan rediyon Ibadan

Daga WAKILINMU

‘Yan daba sun kai hari a wani gidan rediyon da ke Ibadan mai suna Fresh FM, yayin da tashar ke tsaka da gabatar da wani shiri na kai tsaye a safiyar yau Lahadi.

Bayanai sun nuna ‘yan daban sun kai hari tashar ne inda suka sace wasu muhimman kayayyakin aiki da suka haɗa da kwamfutoci, wayoyi da wasu kayayyaki mallakar ma’aikatan gidan rediyon.

Ɗaya daga cikin ma’aikatan gidan rediyon ya shaida wa jaridar Punch cewa, da misalin ƙarfe 6:30 na safiyar wannan Lahadin ɓarayin suka antayo musu.

Ya ƙara da cewa, babu hasarar rai kuma babu wanda ya ji rauni sakamakon harin in banda muhimman kayayyaki da suka kwashe.

Ya zuwa haɗa wannan rahoto, an kasa samun jami’i mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Oyo, Adewale Osifeso, balle a ji ta bakinsa kan lamarin.