’Yan sanda sun bankaɗo shagon ajiye makaman ’yan fashi a Abuja

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta bayyana cewa wani shagon sayar da kayan sawa da ke unguwar Jabi a Abuja na da alaƙa da wata ƙungiyar masu fashi da makami da ake zargi da adana bindigogi da sauran muggan makamai da suke amfani da su wajen aikata laifuka a Suleja da wasu yankunan da ke makwabtaka da ita.

Bayanan da rundunar ta fitar sun nuna cewa binciken ya fara ne bayan kama wani mutum mai suna Bitrus James, wanda aka cafke yayin da yake ƙoƙarin tserewa da wata babur da aka sace bayan wani harin fashi da aka kai a yankin Rafin Chinaka da ke Maje, a ƙaramar Hukumar Suleja.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce kama wanda ake zargin ya taimaka wajen gano wasu mambobin ƙungiyar, lamarin da ya kai jami’an tsaro ga gano alaƙar da ke tsakanin masu laifin da wasu mutane a Abuja.

A cewarsa, jami’an tsaro sun kama mutum tara da ake zargi da hannu a laifukan fashi da makami, satar babura da kuma kisan kai. Waɗanda aka kama sun haca da Aminu Ibrahim daga Jabi a Abuja, Gali Ibrahim Abubakar da Ibrahim Idris daga titin Kaduna a Suleja, Samaila Nasiru daga Jabi, Mohammed Sani daga titin Kaduna, Dorcas Thomas da Rejoice Samaila daga Durumi a Abuja, da kuma Musa Lawal daga Sabon-Wuse.

SP Abiodun ya bayyana cewa binciken farko ya nuna Samaila Nasiru ne ke kula da shagon kayan da Aminu Ibrahim ya mallaka a Jabi, kuma ana zargin ana amfani da shagon wajen ɓoye bindigogi da sauran makamai masu haɗari da ƙungiyar ke amfani da su wajen aikata laifuka.

Ya ce yayin gudanar da bincike, Bitrus James ya bayyana sunayen Aminu Ibrahim da wasu mutum biyu a matsayin mambobin wata ƙungiyar da ta ƙware wajen kwace babura da sauran kayayyaki masu daraja daga hannun jama’a a Suleja, Kwamba da sauran yankuna da ke kusa.

“Bayan bayanan da wanda ake zargin ya bayar, jami’an tsaro sun samu nasarar kama wasu mutum takwas da ake zargi da hannu a laifukan,” inji shi.

Rundunar ta kuma ce bincike ya nuna cewa Rejoice Samaila ta bai wa Bitrus James mafaka a gidanta da ke Durumi, yayin da ake zargin Dorcas Thomas da bayar da bayananta domin taimaka masa wajen buɗe asusun banki da ake zargin ana amfani da shi wajen gudanar da mu’amalolin kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya.

A cewar SP Abiodun, bayanan da ke hannun ’yan sanda sun nuna cewa an gudanar da mu’amaloli masu yawa a cikin asusun bankin.

Binciken farko ya kuma danganta Bitrus James, Aminu Ibrahim, Gali Abubakar, Ibrahim Idris da wasu mutum biyu da har yanzu suke tsere da wata ƙungiyar masu fashi da makami da ake zargi da addabar Suleja da wasu al’ummomin da ke kewaye da ita.

Rundunar ta ce Bitrus da Aminu sun amsa cewa suna cikin ƙungiyar da ta kai hari ga wani Alhaji Monsa a ranar 31 ga Mayun 2026 da misalin ƙarfe 3:00 na dare a bayan Niger Motel, inda aka yi zargin sun caka masa wuka tare da ƙwace masa babur da jaka.

Haka kuma, jami’an tsaro sun kama Musa Lawal, wanda ake zargi da karɓar baburan sata. Ya amsa cewa yana karɓar baburan da aka sace daga hannun Bitrus, Aminu da Ibrahim Idris, sannan ya miƙa su ga Mohammed Sani domin kai su ga masu saye a jihohin Katsina, Kaduna da sauran wurare.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta ce tana ci gaba da farautar sauran mambobin ƙungiyar da suka tsere, tare da ƙoƙarin gano da kuma ƙwato ƙarin kadarorin da aka sace.

By ukarofi

Leave a Reply