
Daga Umar Garba a Katsina
Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa jami’anta sun kama wasu mutane biyu da ake zargin suna kai wa masu garkuwa da mutane makamai a jihohin Kaduna, Katsina da kuma Zamfara.
Kakakin rundunar, Mansir Hassan ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai.
“A ranar 24 ga Ogasta, 2024 jami’an ƴan sanda sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu wajen samar da makamai da alburusai ga masu garkuwa da mutane da ke ta’addanci a jihohin Kaduna, Katsina da kuma Zamfara”. Inji Sanarwar.”
Kakakin, ya ƙara da cewa rundunar ta kuma kama wasu ɓarayin shanu biyu bayan da jami’an ƴan sandan suka daƙile wani yunƙurin garkuwa da mutane a jihar.
Sanarwar ta ce, an ƙwato bindiga ƙirar AK-47 da harsashi biyar daga hannun ƴan bindigar.
ASP Hassan ya bayyana Zahiru Liman mai shekaru 47 da Sani Abdullahi Maƙeri mai shekaru 45, a matsayin waɗanda ake zargi da laifin yunƙurin garkuwa da wasu mutane a jihar Kaduna.
A yayin da sanarwar ta bayyana cewa, Aminu Saleh mai shekaru 25 da Jafar Ibrahim mai shekaru 24 su kuma ana zarginsu da satar shanu.
An kama mutanen ne bayan da wani sahihin rahoton sirri da rundanar ta samu.
ASP Hassan ya ce, ɓarayin shanun na da hannu wajen satar shanun manoma a Kasuwan Magani da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar ta Kaduna.
A lokacin da ake yi wa waɗanda ake zargin tambayoyi game da laifukan da ake tuhumarsu, dukkkansu sun amsa laifukan.
