Hukumar NAPTIP ta ceto yarinya yar shekara 7 a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Hukumar hana fataucin bil’adama ta Ƙasa reshen jihar Katsina ta samu nasarar ceto yarinya da aka kaita aikatau a birnin Abuja tun tana da shekaru 7 da haihuwa.

Wata takardan sanarwar ɗauke da sa hannun shugaban hukumar na jiha, Musa Aliyu Haɗeja ya ce yarinyar ƴar ƙaramar hukumar Malumfashi ne a jihar Katsina.

Ya bayyana cewa, hukumar ta miƙa yarinyar ga iyayenta tare da bata tallafi na kanya ɗinki domin ta koyi sana’a.

Alhaji Aliyu Haɗeja yayi kira ga iyaye suyi ƙoƙarin bai wa ƴaƴansu ilimi da tarbiyya mai kyau da kuma koya mu su sana’a wanda haka zai kautar da su daga irin wannan dabi’a.

Ya nuna fargaban cewa irin wannan aikatau da ake tilastawa yara saboda kwaɗayin abin duniya ke sanya yarinya faɗawa karuwaci.

By Babaji