Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar ‘yan sanda sun kama Muhammad Lawal ɗan shekara 30 da haihuwa ɗauke da miyagun ƙwayoyi 1220 a ƙaramar hukumar Rimi.
‘Yan sanda da ke ƙarkashin ofishin garin Rimi sun kama wannan matashi ne a hanyar Tsagero bayan samun bayanan sirri a kan matashin da ake zargi.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana cewa ‘yan sandan a yayin da suke gudanar da bincike,sun gano yana ɗauke da ƙwayar Exol 5 guda 1000 da D5 guda 200 sai fakiti 10 na Pregablin da kuma fakiti 10 na Tramadol har ma da kuɗi naira 128,800 da ake zargi na cinikin miyagun ƙwayoyi ne.
Muhammad Lawal da ake zargi ya tabbatar da cewa waɗannan ƙwayoyi da aka kama tasa ce, kuma yana kan hanyar sa na zuwa raban kwayoyin ga mutane sa a sassar ƙaramar hukumar ta Rimi.
DSP Abubakar Sadiq ya sanar da cewa da zarar ‘yan sanda sun kammala bincike za a gabatar da shi kotu.
CP Ali Umar Fage ya jinjinawa jami’an sa kan ƙoƙarin da suke na yaƙi da ɓatagari. Ya tabbatar wa al’ummar jihar Katsina cewa za su cigaba da kama masu tammali da miyagun ƙwayoyi har ma da sauran ɓatagari a jihar.
