Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar ‘yan sanda a Katsina ta sami nasarar kama wani mai suna Sunday Eze da aka fi sani da suna Danbuje da ke kai wa yan bindiga miyagun ƙwayoyi a ƙaramar hukumar Funtua.
A cewar jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu, Danbuje ya zo hannu bayan da jami’an ‘yan sanda a Funtua suka sami bayanan sirri game da wannan ƙasurgumin dillalin ƙwayoyi a garin na Funtua.
Ya bayyana cewa a lokacin da ‘yan sanda suka kama Danbuje yana ɗauke da ƙwaya 500 na D5 a tare da shi.
DSP Abubakar Sadiq ya ce ‘yan sanda za su cigaba da bincike har su gano daga inda yake samo da wurare da yake raba irin wannan ƙwayoyi Kuma da zaran an kammala bincike za a turo shi kotu.
Kwamishinan ‘yan sanda CP Ali Umar Fage ya roƙi alummar jihar da su taimaka wa jami’an tsaro wajen bada bayanai na sirri kan maɓoyar irin waɗannan miyagun mutane.
