‘Yan sanda sun kashe ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja, Dogo Saleh

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƴan sanda a Abuja, sun samu gagarumar nasara a ƙoƙarinsu na daƙile ayyukan ta’addanci a babban birnin, inda suka kashe shahararren mai garkuwa da mutane, Dogo Saleh.

Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta faɗi hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, inda ta tabbatar wa mazauna yankin cewa jami’ansu na aiki tuƙuru wajen magance ƴan ta’adda da ayyukansu a birnin da ma maƙota jihohi.

Ta ce, sun kashe ɗan bindigar ne bayan samun wani rahoton sirri, sakamakon ayyukansa na ta’addanci da garkuwa da mutane a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, Lokoja da Enugu da ma cikin ƙwaryar birnin.

Jami’an sun bi diddigin Salisu Mohammed ne mai shekaru 21 da aka fi sani da Dogo Saleh akan hanyarsa ta zuwa ƙaramar hukumar Bwari.

An kuma gano cewa, Dogo Saleh ya na yi wa jagororin ƴan bindiga a Kaduna aiki waɗanda ke gudanar da ayyukansu a yankin dajin Rijana dake Jihar Kaduna.

Ya kuma ƙware wajen yin garkuwa da mutane a manyan titina da karɓar maƙudan kuɗaɗen fansa daga waɗanda suka shiga komarsa.

Kazalika, a yayin kama shi ya yi ƙoƙarin tserewa, lamarin da bai yiwu ba, inda ya bar kayayyakin da suka haɗa da bindiga ƙirar AK47 da mazubin harsasai guda biyu da alburusan 7.62mm guda 60 da kuma tsabar kuɗi kimanin Naira miliyan uku.

By Babaji