‘Yan sanda sun kashe ƙasurgumin ɗan bindiga a Kaduna

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Rundunar ‘yan sanda ta babban birnin tarayya (FCT) ta ce ta kashe wani da ake zargin ƙasurgumin ɗan bindiga yayin wani musayar wuta a dajin Kwasau, jihar Kaduna.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta FCT, SP Josephine Adeh, ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Abuja ranar Laraba, inda ta ce an kashe wanda ake zargi ne sakamakon wani aikin leƙen asiri da aka tsara sosai don yaƙar satar mutane da kuma karya lagon masu aikata miyagun laifuka a babbar hanyar Kaduna-Lokoja-Enugu.

Ta ce, bayan samun sahihin bayanai game da motsin ‘yan bindigan zuwa birnin tarayya a ranar 3 ga Maris, shugaban sashin yaƙi da satar mutane ya jagoranci jami’an tsaro don toshe hanyoyin da ake amfani da su. Daga bisani an yi nasarar kama wani wanda ake zargi a dajin Gidan Abe, yayin da yake kan hanyarsa zuwa Bwari.

SP Adeh ta bayyana cewa wanda aka kama ya amsa cewa shi ne babban mai harbi na shugabannin ‘yan bindigan da ke aiki a dajin Rijana, Kaduna, inda suke addabar al’ummomi da garkuwa da mutane tare da karbar kuɗin fansa mai yawa.

A ranar 4 ga Maris, da misalin ƙarfe 11:14 na dare, bayan samun ƙarin bayanai daga wanda ake zargi, jami’an suka ƙaddamar da wani samame zuwa dajin Kwasau da ke Kagarko, Kaduna. A can ne ‘yan sanda suka yi arangama da wasu ‘yan bindiga da suka yi yunƙurin kuɓutar da abokin aikinsu, amma jami’an suka nuna bajinta tare da yin nasara a kan ‘yan bindigan da suka tsere da raunuka masu tsanani.

Bayan kammala musayar wuta, wanda ake zargi ya samu munanan raunuka daga harbin abokan aikinsa, inda daga bisani aka garzaya da shi asibitin Kubwa General Hospital, inda aka tabbatar da mutuwar shi.

By ukarofi