Tinubu ya gana da ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Legas

Spread the love

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da wasu mambobin Majalisar Dokokin Jihar Legas a fadar shi da ke Abuja a ranar Laraba da yamma. ‘Yan majalisar sun isa wajen taron cikin motoci guda biyu sannan suka jira a ofishin shugaban ƙasa kafin fara ganawar.

Daga cikin manyan ‘yan majalisar da suka halarta akwai shugaban majalisar, Hon. Mudashiru Obasa, da tsohuwar shugaban majalisar kuma mataimakiyar shugaban yanzu, Hon. Mojisola Meranda.

Ganawar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rikicin shugabanci a Majalisar Jihar Legas. A lokacin isowar su, Meranda da wasu mambobin majalisar sun iso wajen taron da misalin ƙarfe 2:00 na rana, yayin da Obasa ya iso daga baya da misalin karfe 2:50 na rana.

Ana hasashen cewa tattaunawar ta mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi rikicin da ya yi sanadin cirewa da dawowar Obasa a matsayin shugaban majalisar.

By ukarofi