
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Laraba ne wani abu mai kama da wasan kwaikwayo ya faru Ribas, inda Gwamna Siminalayi Fubara ya je zauren Majalisar Dokokin jihar inda ya tarar da ƙofar shiga a kulle.
Rahotanni sun bayyana cewa, jami’an tsaro ne suka kulle ƙofar a lokacin da tawagar gwamnan ta isa zauren.
Jami’an sun ce sun yi hakan ne saboda ba a samu wani saƙo ko tattaunawa ta musamman a tsakanin gwmnan da majalisar ba.
Saidai, Gwamna Fubara ya ce ya aika saƙo zuwansa ga Kakaki Martins Amaewhule da kuma ƙoƙarin kiran sa ta waya tun a ranar Talata.
Fubara ya ce, zai aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli na ranar 28 ga watan Fabrairu da kuma umartar Hukumar zaɓe ta jihar da ta shirya gudanar da sabon zaɓe.
Haka kuma, a wani saƙo da ya fitar a ranar 7 ga watan Maris, Sakataren gwamantin jihar Tammy Danagogo ya nemi ganawa da ƴan majalisar da nufin tattauna sake gabatar da kasafin 2025 a yanayi na lumana.
Saidai, majalisar ta nemi gwamnan ya gabatar da takardar gayyatar ta hanyoyin da suka dace, inda daga baya suka ƙi amsa gayyatar da gwamnan ya yi masu.
Hakan ya faru ne sa’o’i 24 da Shugaba Bola Tinubu ya umarci Fubara da ya aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli.
