
Daga BELLO A. BABAJI
Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shatima ya bayyana hakan a yayin da ya karɓi baƙoncin takwaransa Mataimakin Shugaban ƙasar Brazil, Geraldo Alckmin don tattaunawa kan yadda za a sabonta dabarun cin gajiyar dangantaka tsakanin Nijeriya da Brazil.
Tawagar ta Brazil ta haɗa manyan jagorori a ɓangarorin gwamnati da masu zaman kansu na ƙasar.
Baƙin sun biyo sawu ne sakamakon tsaikon da aka samu a ɓangaren zartar da yarjejeniyoyin da aka cimma na tsawon shekaru.
A jawabinsa, Kashim Shatima ya bayyna cewa, Shugaba Bola Tinubu mutum ne wanda ya nuna ƙwarewa da jajircewa wajen samar wa ƴan Nijeriya kyakyawan ci-gaba,
inda ya ce a yanzu haka Nijeriya tana kan sabon tafarkin ci-gaba, da kuma Samar da sabbin tsare-tsare a fannin zuba jari a ɓangarori daban-daban domin samar da gobe mai inganci ga matasa.
Kashim ya kuma yi kira ga ministocin da suka samu halartarr taron da su yi shiri sosai domin samar da sauye sauye da dabaru da za su amfani ƴan Nijeriya don kai wa i’zuwa ga mataki na gaba.
